2023: Kotu ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaben Shugaban Kasa

Hakan ya biyo bayan yanke hukuncin karshe da kotun ta yi ranar Laraba

2023: Kotu ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaben Shugaban Kasa

Kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa Bola Tinubu ne ya lashe sakamakon zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairun da ta gabata.

Alkalan kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani ne ya tabbatar da haka bayan ya je hukuncin karshe a zaman kotun na ranar Laraba.

Kotun ta kuma ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi daidai da ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

A cewar kotun, wadanda suka shigar da karar sun gaza gabatar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da da’awarsu.

Mai Shari’a Tsammani ya ce, “Hujjojin da da masu shigar da kara suka gabatar da kwarara ba ne. A kan haka, ina tabbatar da nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a matsayin sahihin zababben Shugaban Najeriya.”

Kotun ta kuma yi fatali da hujjoji 37 da shaidu suka gabatar a gabanta.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta