2023: Kwankwaso ya zama dan takarar Shugaban Kasa na NNPP
Ya zama dan takarar jam’iyyar ne ba tare da hamayya ba
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zama dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP ba tare da hammaya ba.
Ya zama dan takarar ne bayan ya lashe zaben fitar da gwanin da ya gudana a Abuja ranar Laraba.
- Babu wanda na kullata a cikin wadanda suka yi takara da ni – Tinubu
- Aisha Buhari ta fice daga taron APC a fusace
Kwankwaso, wanda tsohon Ministan Tsaro ne shi kadai ne yake takarar a cikin jam’iyyar, kuma daliget dinta sun taru inda suka amince da shi a matsayin dan takarar.
An dai gudanar da taron ne a dakin taro na filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.
A cewar Shugaban jam’iyyar ta NNPP na kasa, Dokta Boniface Aniebonam, yayin zantawarsa da manema labarai a Abuja, taron an gudanar da shi ne don a tabbatar da Kwankwason a matsayin dan takarar jam’iyyar a hukumance.
“Shi (Kwankwaso) an zabe shi ne a matsayin dan takara ba tare da hamayya ba. Kwankwaso mutumin kirki ne,” inji Shugaban jam’iyyar.