2023: Me ya sa sanatocin APC ke ficewa zuwa wasu jam’iyyun?
Masana na ganin hakan zai iya yin illa ga jam’iyyar
- Ficewarsu na damuna matuka—Abdullahi Adamu
- Dalilin da ke jawo ficewar sanatocin—Dokta Dukawa
A ranar Talata, 22 ga Yunin bana ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zauna da sanatocin Jam’iyyar APC su 22 da suka yi yunkurin ficewa daga jam’iyyar saboda abin da suka kira cewa ba a yi musu adalci ba a zaben fid-da-gwanin jam’iyyar.
Rahotanni sun ce akalla akwai shari’o’i 75 da jam’iyyar ke fuskanta a yanzu, kuma mafi yawa sanatoci ne da ’yan Majalisar Wakilai abin ya shafa.
- Yawan mutanen duniya zai kai biliyan 8 kafin karshen 2022 – MDD
- Harin Gidan Yarin Kuje: An kama fursuna daya a wata tashar mota a Abuja
A zaben fid-da-gwanin da aka yi, da yawa daga cikin sanatocin APC da ’yan Majalisar Wakilai sun fadi a jihohinsu.
Duk da cewa wadansu daga cikinsu suna da wasu hujjojin daban, amma Aminiya ta gano mafi yawansu sun yi yunkurin ficewa daga jam’iyyar ce saboda sun fadi zaben fid-da-gwani.
Duk da yunkurin hana su ficewar, jam’iyyar ta rasa sanatoci akalla takwas kamar Malam Ibrahim Shekarau na Kano da Yahaya Abdullahi da Adamu Aliero duka daga Jihar Kebbi da Dauda Jika da Lawal Yahaya Gumau daga Bauchi da Ahmad Babba Kaita na Katsina da Francis Alimikhena na Jihar Edo da Godiya Akwashiki na Jihar Nasarawa.
Yanzu haka APC na da sanatoci 60 ne a Majalisar Dattawa, NNPP na da uku, YPP na da biyu, Labour Party daya ita ma APGA daya.
Idan aka ci gaba da samun sanatoci suna ficewa, za su iya kawo cikas ga ayyyukan Shugaban kasa kasancewar APC na bukatar akalla biyu bisa uku na sanatocin domin jan akalar majalisar.
Bayan ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadansu daga cikinsu sun bayyana gamsuwarsu, akalla na dan lokaci, inda suka amince su ci gaba da zama idan an yi abin da ya dace.
Shi kuma Shugaba Buhari ya ja hankalinsu su tsaya su taimaki jam’iyyar ta samu nasara.
Dalilan sanatocin na ficewa Sanata Francis Alimekhena mai wakiltar Edo ta Arewa ya ce rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a jiharsa ne ya sa ya fice.
Sai dai Aminiya ta gano a zaben fidda-gwanin APC a jihar, tsohon Gwamnan Jihar, Kwamared Adams Oshiomhole ne ya doke shi, wanda hakan ya sa ya fice.
Sanatan Shugaba Buhari, Sanata Ahmed Babba Kaita shi ma ya sanar da ficewarsa ce bisa dalilin rashin sa shi a cikin harkokin jam’iyyar, wanda hakan ya sa ya koma PDP.
Shugaban Masu Rinjaye, Sanata Yahaya Abdullahi da tsohon Gwamnan Jihar Kebbi ne suka fi girgiza jam’iyyar, inda suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar tare da magoya bayansu.
Sun zargi Gwamnan Jihar da sa jam’iyyar a aljihunsa ta hanyar yin abubuwa ba tare da sa su a ciki ba.
Takarar Shugaban Majalisar Dattawa Shi kansa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan yana fuskantar nasa kalubalen, bayan Alhaji Bashir Machina ya ki janye wasa ya yi takarar sanata, bayan ya fadi a zaben dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar.
A kwanaki Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta fitar da sunayen ’yan takarar sanatoci da Jam’iyyar APC ta tura mata kuma ciki akwai sunan Sanata Ahmad Lawan.
Aminiya ta ruwaito wanda ya lashe zaben fid-da-gwani na Sanatan Yobe ta Arewa, Alhaji Bashir Machina yana cewa ba zai janye takararsa ba, domin a cewarsa shi ya lashe zaben fid-da-gwanin, don haka bai ga dalilin da zai janye wa Sanata Ahmad Lawan ba.
Ficewarsu na damuna matuka -Abdullahi Adamu
Da yake magana kan batun, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nuna damuwarsa kan yadda sanatocin ke ci gaba da ficewa daga jam’iyyar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan wani taron sirri da sanatocin APC a Abuja a kwanakin baya, Shugaban ya ce abin takaice ne yadda ake ficewa daga cikinta.
Ya ce, “A kowacce shekarar zabe, irin wadannan abubuwa ba sababbi ba ne. Najeriya da APC kuma ba za su zama na daban ba. Saboda haka, ban damu da me ke faruwa a wasu jam’iyyun ba, APC ce a gabana.
“Ba a iya APC hakan ke faruwa ba, amma da yake mu ne jam’iyya mai mulki, shi ya sa matsalarmu ta fi fitowa fili.
“Babu shugaban da ya san abin da yake yi da ba zai damu ba idan ya yi asarar ko da mutum daya, ballantana biyu ko uku,” inji Abdullahi Adamu.
Hamayya da gwamnoni ne ke cin sanatocin-Dokta Dukawa
Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa malami a Tsangayar Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero, Kano ya ce dalilin da ya sa sanatoci ba su komawa kan kujerunsu shi ne bai wuce hamayyar da ke tsakaninsu da gwamnonin jihohinsu ba.
“Za ki ga a mafi yawan lokuta wasu sanatocin mazabarsu daya da wasu gwamnonin musamamn wanda ya gama wa’adin mulkinsa karo na biyu wanda kuma za ki samu a wanan lokaci yana so ya tafi Majalisar Dattawa. A nan ba zai yarda wannan sanata ya koma ba,” inji shi.
Dokta Dukawa ya ce wani dalilin shi ne gwamnonin ba su son su ga sanata ya dade a kan kujera inda zai tara abin duniya ya yi karfi a siyasance don kada ya iya yin hamayya da su a jihohinsu.
“Ba su fiye son sanatoci su yi karfi a siyasance ba, sun fi so mutum ya dana sau daya ko sau biyu ya sauka. A nan za su sa wani sabo ya je wajen wanda bai yi karfin da zai iya gogayya da su a siyasance a jihohinsu ba. Wannan shi ne bababn dalilin da ya sa ba su fiye tunanin wai ko sanatan yana amfana wa al’umma ko ba ya amfanawa a jihohinsu ba,” inji shi.
‘Abin da ya sa wasu suke dadewa’
Masanin siyasar ya kara da cewa, “Idan har aka ga sanata ya dade ainun to za a samu cewa bai hada mazaba da wani gwamna da ke bukatar wannan kujerar tasa ba. Ko kuma za a samu cewa sanatan yana yi wa gwamnan hidima ta fitar hankali.
“Ma’ana dai zai zama kamar sayen wannan kujera yake yi duk lokacin da zabe ya zo. Abu na uku kuma shi ne bai yi rashin sa’ar samun wani makusancin gwamnan da yake son wannan kujera ba.
“Idan da an samu wani makusancin gwamnan yana son kujerar, to fa komai kudin da yake kashewa wajen sayen kujera duk da haka ba zai samu dama ba.”
‘Sanatocin za su iya cikas ga jam’iyyar’
Game da tasirin sanatocin a zabe mai zuwa, Dokta Dukawa cewa ya yi ire-iren wadannan sanatoci da suka rasa kujerunsu suna da tasiri sosai a zabe domin idan ba a yi sa’a ba, za su iya kawo wa jam’iyya cikas a zaben.
“Babu shakka ire-iren wadannan sanatoci da ba su samu tikitin takara ba, za su iya raunata jam’iyya gwargwadon karfinsu da kuma mutuncinsu.
“Ko su fice daga jam’iyyar tare da komawa wata jami’yyar wanda kuma hakan rauni ne ga jam’iyya domin a siyasa ko da mutum daya jam’iyya ba ta so ta rasa ballantana sanata sukutum tare da jama’arsa.
“Ko kuma ya ci gaba da zama a cikin jami’yyar ya kuma yi mata kafar ungulu a wani abu da aka fi sani da antiparty a Turance wato yana cikin jam’iyyar amma ya sa a zabi wata jam’iyyar daban,” inji Dokta Dukawa.