2023: Peter Obi ne dan takarata —Obansajo
Obasanjo ya ce Peter Obi ya yi wa sauran ’yan takarar shugaban kasa fintinkau wajen ilimi da kwarewa.
A karon farko tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya fito bainar jama’a ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, a zaben 2023.
Da yake bayyana goyo bayan nasa a cikin sakonsa na murnar shiga Sabuwar Shekarar 2023, Obasanjo ya ce Peter Obi ya yi wa sauran ’yan takarar shugaban kasa fintinkau wajen ilimi da kwarewa.
- 2023: Peter Obi ne dan takarata —Obansajo
- Akwai yiwuwar mazauna karkara su sha wahalar canjin kudi a 2023 – Masani
A cikin sakonsa nasa mai mai taken, “Rokona ga ’yan Najeriya, musamman matasa,” Obasanjo ya ce, “Duk da cewa a cikin masu masu takarar babu wani shafaffe da mai, amma a cikin Peter Obi ya fi sauran nagarta ta bangaren kyawun dabi’u, gogewa, fahimta, abin da suka yi a baya da wanda za su iya kawowa.”
“Sauran kuma, kamar kowannenmu na da irin gudunmawar da zai bayar a sabuwar gwamantin wajen farfado da al’amura da kuma ceto Najeriya.
“Dadin dadawa, Peter Obi allura da zare ne mai wuyar bata ga al’ummar Arewaci da Kudancin Najeriya, saboda da masu fada masa magana ya ji, idan bukatar hakan ta taso.
“Sannan yana da mataimaki wanda matsashi ne mara tabo a bangaren nasarorin da ya samu a rauyuwa, da kuma harkokin jama’a,” in ji sakon na Obasanjo.