2023: Sha’aban Sharada ya koma ADP don yin takarar Gwamnan Kano
Tuni ya sayi fim din takarar Gwamna a jam’iyyar
Dan majlisar Tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Birni da ke Kewaye a jihar Kano, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya fice daga jam’iyar APC zuwa ta ADP.
Wani makusancin dan majalisar ne ya bayyana hakan ga wakilinmu, inda ya ce har ma ya sayi tikitin takarar Gwamnan Kano a jam’iyar, kuma ya dauki Rabiu Bako a matsayin Mataimakinsa.
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 9, ya jikkata 13 a Bauchi
- Motar bas makare da ’yan sanda ta fada kogi a indiya
Duk da bai bayyana dalilin barin tsohuwar jam’iyar tasa ba, bayanai na nuna rashin sanin makomarsa a cikinta ne ya sanya shi hakan.
Idan za a iya tunawa dai, a baya Sha’aban din da ake yi wa kirari da ‘Sauro’ ya sha samun sabani da shugabancin APC tsagin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bisa bambamcin ra’ayin siyasa.
A baya ya fito takarar Gwamna a tsohuwar jam’iyyar tasa, sai dai bai yi nasara ba, inda Mataimakin Gwamna mai ci, Nasiru Yusuf Gawauna ya lashe kujerar a zaben mai cike da rudani.
Daga baya dai Sha’aban ta shafukansa na sada zumunta, ya bayyan rashin gamsuwarsa da zaben, inda ya ce har a filin zaben ma tsagin Gwamnan sun masa barazanar kashe shi, baya ga hana dogaransa rako shi harabar zaben, da kuma kai wa magoya bayansa hari.
To sai dai uwar jam’yar ta yi watsi da wannan ikirari na dan majalisar, inda ta ce ya gabatar da hujjoji kan maganganun nasa ga kwamitin karbar korafe-korafen zabe na jam’iyar, domin daukar matakan da suka dace.