2023: Su Yakubu Dogara da wasu ’yan APC sun yanke shawarar goyon bayan Atiku
Sun ce ba su gamsu da takarar Musulmai biyu ba a APC
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da wasu ’yan jam’iyyar APC da ba su gamsu da takarar Bola Tinubu ba sun yanke shawarar goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar na PDP.
Sun ce bayan gudanar da zuzzurfan nazari kan halin da kasar ke ciki, Kiristocin Arewacin Najeriya sun yanke shawarar yin aiki tare da takawarorinsu Musulmai su goyi bayan dan takarar da zai kayar da Musulmai biyun da APC ta tsayar.
- Sojoji sun sake kashe mayakan ISWAP da dama a Borno
- 7 daga cikin kowane yaro 10 a Jigawa na rayuwa cikin kangin talauci – UNICEF
Da yake gabatar da rahoton kwamitin da suka tattara kan ’yan takarar Shugaban Kasar, tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba, ya ce sun amince su dauki Atikun ne bayan la’akari da shawarwarin da Shugabanninsu suka ba su.
Wadanda suka halarci taron kaddamar da roahoton sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Idris Wada da tsohon Ministan Albarkatun Ruwa, Mukhtar Shagari da sauransu.
Rahoton dai na dauke ne da sa hannun Shugaban kwamitin, kuma tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Mohammed Kumalia da Sakatarensa, Barista Mela Nunge.
A cewar Simon Achuba, kwamitin ya yi nazarin a kan dan takarar APC, Bola Tinubu da na LP, Peter Obi da na NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, bayan shi Atikun.
Sai dai ya ce sun yanke shawarar mara wa Atikun baya ne saboda jam’iyyarsa ta PDP ta fi yaduwa a fadin Najeriya fiye da NNPP ta Kwankwaso da kuma LP din Peter Obi.