2023: Tirka-tirkar da Gwamnoni 17 ke sha a kokarin tsayar da magadansu

Takaddama ta turnike yunkurin da wasu Gwamnoni 17 masu barin gado suke yi na nada wadanda za su gaje su gabanin zaben fid da gwani na Gwamnonin a jam’iyyun APC da PDP. Rahotanni da Aminiya ta tattaro daga jihohin da lamarin ya shafa sun nuna kokarin da Gwamnonin ke yi na ganin cewa sun nada […]

2023: Tirka-tirkar da Gwamnoni 17 ke sha a kokarin tsayar da magadansu

Takaddama ta turnike yunkurin da wasu Gwamnoni 17 masu barin gado suke yi na nada wadanda za su gaje su gabanin zaben fid da gwani na Gwamnonin a jam’iyyun APC da PDP.

Rahotanni da Aminiya ta tattaro daga jihohin da lamarin ya shafa sun nuna kokarin da Gwamnonin ke yi na ganin cewa sun nada madagansu ya ta da kura a manyan jam’iyyun biyu.

Akalla ’yan takara 201 ne suka yanki tikitin takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar APC yayin da jam’iyyar ta tsayar da 26 ga Mayun bana a matsayin ranar zaben fid da gwani.

Sannan a bangaren PDP, ’yan takara 145 ne za su fafata a zaben fid da gwanin takarar Gwamna wanda jam’iyyar ta za gudanar a ranar 25 ga watan da muke ciki.

Jihohi 29 ne ake sa ran Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamnoni a 2023, yayin da ragowar jihohi bakwai ba sa daga cikin wannan tsarin.

Gwamnonin APC da PDP da suka yi tsayin daka wajen ganin sai nasu ne zai gaje su a zabe mai zuwa sun hada da, Okezie Ikpeazu (Abia) da Emmanuel Udom (Akwa Ibom) da Samuel Ortom (Binuwai) da Ben Ayade (Kuros Riba) da Ifeanyi Okowa (Delta) da Dave Umahi (Ebonyi) da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) da Mohammed Badaru Abubakar (Jigawa) da kuma Nasir El-Rufai (Kaduna).

Sauran gwamnonin sun hada da Abdullahi Umar Ganduje (Kano) da Aminu Bello Masari (Katsina) da Atiku Bagudu (Kebbi) da Abubakar Sani Bello (Neja) da Simon Lalong (Filato) da Nyesom Wike (Ribas) da Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) sai kuma Darius Ishaku  na Jihar Taraba, wadanda dukkaninsu sun kammala wa’adinsu na biyu ke nan.

A hannu guda, Gwamnonin manyan jam’iyyun su 11 da ke fafutukar ganin sun tsallake siradi zuwa wa’adin mulki na biyu, akwai Ahmadu Fintiri (Adamawa) da Bala Mohammed (Bauchi) da Babagana Zulum (Borno) da Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe) da AbdulRahman AbdulRasaq (Kwara) da Babajide Sanwo-Olu (Lagos) da Abdullahi Sule (Nasarawa) da Dapo Abiodun (Ogun) da Seyi Makinde (Oyo) da Mai Mala Buni (Yobe) hade da  Bello Matawalle  na Jihar Zamfara.

Uba Sani ne zabin El-Rufai

’Yar manuniya ta nuna cewa a Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani na APC mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya shi ne wanda Gwamna El-Rufa’i yake fatan ya zama dan takarar Gwamna na APC a Jihar.

Matakin Gwamnan ya biyo bayan ganin yadda sauran ’yan takarar suka lale kudi har naira miliyan 50 kowannensu wajen sayen fom din bayyana ra’ayin tsaya wa takara don neman gaje kujerarsa bayan kammala wa’adinsa a 2023.

Masu sa ido kan al’amuran APC sun ce, duk da dai Gwamnan na da karfin jujjuya jam’iyyar, amma matakin da ya dauka ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar.

Domin kuwa, tsohon dan Majalisar Wakilai kuma mai neman takarar gwamna karkashin tutar APC, Alhaji Sani Mahmud Sha’aban, ya bayyana matakin da El-Rufai ya dauka a matsayin cin mutuncin Dimokuradiyya.

Sha’aban, wanda dansa Turad ke auren diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Hannan, ya yi ikirarin cewa shi ne mutum na farko da ya sayi fom din bayyana ra’ayin neman takara a Jihar.

Don haka ya ce yana da tabbacin cewa Shugaban Kasa da ma shugabannin jam’iyyarsu ta APC ba za su lamunci tsarin nan na dauki-dora ba.

Ana adawa da zabin Ortom a Binuwai

A Jihar Binuwai ma ba ta sake zani ba, don kuwa tuni Gwamna Samuel Ortom ya nuna babu wanda ya cancanci ya zama magajinsa irin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Titus Uba.

Kodayake dai, an ce da farko ba Uba ne zabin Ortom ba duk da cewa suna dasawa.

Ana zargin cewa Ortom ya yanke shawarar yi da Uba bayan da Shugaban PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu ya nuna masa falalar da ke tattare da hakan, an ce tuni Gwamnan ya aminta da hakan ya kuma bukaci mabiyansa su goya masa baya, lamarin da aka ce bai yi wa wasu ’yan PDP a Jihar dadi ba.

Yayin da wasu ’yan takarar suka bi zabin Gwamnan, wasunsu kuwa murtuke fuska suka yi suka nuna rashin yardarsu da zabin nasa.

Wannan mataki ya sanya wasu ficewa daga jam’iyyar ba tare da wani jinkiri ba, sannan wasu na jiran ganin yadda za ta kaya a zaben fid da gwanin da PDP za ta gudanar.

Akwai yamutsi a Akwa Ibom

A Jihar Akwa Ibom kuwa, PDP ta ce sam bata amince da yunkurin da Gwamna Udom Emmanuel ya yi ba na neman tsayar da Fasto Umo Eno a matsayin wanda zai gaje shi.

Emmanuel ya ce ya zabi Umo Eno ne saboda ya gamsu da cewa zai iya dorawa daga inda zai tsaya wajen ciyar da jiharsu gaba. Tare da bayyana shi a matsayin “mutum wanda ake girmamawa kuma mai kwarewa.”

Sai dai, sauran ‘yan takarar gwamna a jihar daga mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas wadan tsarin karba-karba ya nuna cancantarsu, na ra’ayin a matsayinsu na ‘yan jam’iyya, suna da ‘yancin su yi zabe a kuma zabe su.

Daya daga cikin wadannan ‘yan takara shi ne, Sanata Bassey Akpan, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Sha’nin Hako Fetur a Tudu na Majalisar Dattawa, ya yi zargin akwai yarjejeniyar baka da suka yi kan cewa Gwamna Emmanuel zai mika masa mulki a 2023.

Shin hakar Umahi za ta cimma ruwa a Ebonyi?

Kakakin Majalisar Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ne zabin Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi a matsayin wanda yake so ya gaji kujerarsa a 2023.

Sai dai wannan mataki da Gwamnan ya dauka ya haifar da mummunan rarrabuwar kai a tsakanin mambobin tsohuwa da sabuwar APC a jihar.

Wakilinmu ya gano cewa tsofoffin mambobin jam’iyyar wadanda suke jin cewa ba a yi da su, sun kai korafinsu gaban uwar jam’iyya ta kasa don ta sa baki wajen kashe wutar rikicin.

Zabin Ganduje ya raba kan APC a Kano

A nasa bangaren, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya sanar da matsayarsa ta tsayar da Mataimakinsa Nasir Gawuna ya zama magajinsa a 2023.

Da alama dai wasu ‘yan APC a Kano ba su yi na’am da wannan mataki ba, lamarin da ya yi sanadiyyar ficewar wasu kusoshin APC a jihar, ciki har da tsohon Gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau.

Sauya sheka da Shekarau ya yi ya cimma Rabiu Musa Kwankwaso a sabuwar Jam’iyyar NNPP, hakan ana iya cewa ya sauya makomar siyasar Kano.

Masana harkokin shari’a na ganin cewa, komai na iya faruwa a zaben 2023 duba da yadda NNPP ke ta kara samun tagomashi a Kano da kewaye.

Tuni dai da yawa daga ‘yan Majalisar Jihar Kano suka sauya sheka suka bar APC da PDP zuwa wasu jam’iyyun a jihar.

Bayan janye kudirinsa na neman kujerar sanata, kawo yanzu babu wanda ya san takamammen mukamin da Ganduje zai nema a 2023.

Ana tsumayin wanda Badaru zai ayyana

Rashin sanin wanda Gwamna Muhammad Badaru na Jihar Jigawa zai ayyana a matsayin wanda zai gaje shi a 2023, ya bar mukarrabansa da ma ‘yan jami’yya cikin zulumi a jihar.

Aminiya ta kalato cewa Gwamnan ya sha fada a wajen tarurruka tare da bai wa jama’a tabbacin ba zai sa baki ba wajen zaben wanda zai gaje shi.

Akalla ‘yan siyasa tara ne suka yanki tikitin neman takarar gwamnan a jihar daga jam’iyyarsa, inda uku da cikin ‘yan takarar suka fito daga yankin Hadejia; biyu daga Birnin Kudu; daya daga Dutse: daya daga Jigawa ta tsakiya; daya daga Kazaure, sai kuma daya daga Gumel.

Yiwuwar samun nasara ga Idris bayan janyewar Malami a Kebbi

Alamu daga Jihar Kebbi sun nuna tauraruwar dan Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago (NLC), Nasiru Idris, ita ce tafi ta sauran ‘yan takara haskakawa a APC.

Janyewar kudirin takara da Babban Lauyan Kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi, hakan na shirin bai wa Idris din damar tsintar dami a kala. Domin kuwa, kwararan alamu na nuni da Idris na samun goyon bayan gwamnan jihar.

Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Dokta Yahaya Abdullahi da kuma Abubakar Garry Malami su ne ‘yan takarar da ake sa ran su fafata da Idris a zaben fid da gwani mai zuwa.

An ce tsohon gwamnan jihar, Sanata Adamu Aliero, shi ne kan gaba wajen tallata takarar Yahaya Abdullahi a jihar.

Ayade da Wike da Bello sun bar masoyansu cikin halin kaura-da-ka

Har yanzu, gwamnonin Kuros Riba da Ribas da Neja ba su ce komai ba dangane da zaben wadanda za su gaje su. Lamarin da ya jefa masoyansu cikin halin kaura-da-ka yayin da ya rage ‘yan kawanaki a gudanar da zaben fid da gwani.

Babu wani cikakken bayani kan cewa Gwamna Ben Ayade ya ayyana daya daga cikin ‘yan takara 17 da ake da su a jam’iyyarsa don zama magajinsa. Sai dai, Kwamitin tantancewar da APC ta kafa karkashin jagorancin Sanata Victor Ndoma-Egba, ta fitar da sunayen ‘yan takara hudu da ya tantance.

Haka shi ma Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, an gano cewa har yanzu bai nuwa wanda zai gaje shi ba. Majiyarmu ta ce, da ma dai Gwamnan ya riga ya fada cewa ba zai sa baki ba a sha’anin tsayar da dan takarar dad a zai zama magajinsa face a bar jama’a su zabi wanda suke su.

Ana zaman dar-dar a Ribas

Batun wane ne ya fi cancantar ya ayyana dan takarar da zai gaji Gwamna Nyesom Wike a zaben 2023, ya haifar da dar-dar a tsakanin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP a Jihar Rivers.

Duka ‘yan takara 17 da suka yanki tikitin shiga takara a jihar karkashin tutar PDP, sun tsallake tantancewa in banda mutum guda, wato Dokta Farah Dagogo, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Bonny/Degema a Majalisar Tarayya, saboda kin gabatar da kansa ga kwamitin tantancewar.

Bayanai sun ce, hakan ya faru da dan takarar ne saboda cika hannu da ‘yan sanda suka sa’ilin da ya tafi sakatariyar PDP ta shiyyar Kudu maso Kudu domin a tantance shi kasancewar da ma ‘yan sandan na nemansa ruwa a jallo bisa zarginsa da hannu cikin tarwatsa shirin tantance ‘yan takarar majisar jiha na Majalisar Tarayya.

Amma wasu ‘yan jihar na ra’ayin cewa, zurfin ilimi da matsayin dan takarar ne suka firgita Gwamna Wike shi ya sa, ya sa aka kamo dan takarar. Sannan kuma wasunsu na cewa, babu wanda ya san zabin Gwamnan game da wanda yake so ya gaje shi daga cikin ‘yan takara 16 da suka rage.

Cin mutuncin dimokuradiyya ne  – Kari

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan badakalar, masannin fannin siyasa daga Jami’ar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, ya bayyana ayyana magajinsu da gwamnonin ke yi a matsayin cin mutunci kai-tsaye ga tsarin dimokuradiyya da fatali da ‘yanci ra’ayi wanda yana daya daga manyan shika-shikan da siyasa ke gudana a kansu.

“Jama’a ne kadai, ko kuma misalin mambobin jam’iyya ke da ‘yancin tasayar da dan takara kamar yadda yake kunshe cikin Kundin Tsarin Mulki na 199 da Dokar Zabe ta 2022 da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyu.

“Abin takaici ne yadda gwamnoni suka mallake ikon tsayar da dantakara a jam’iyyu. Ko shakka babu wannan ya nuna yadda gwamnonin suka dauki kansu da mushimmanci bisa ga kan talakawa wanda hakan ya saba wa al’adun dimokuradiyya ta gaskiya,” inji shi.

A nasa bangaren, Barista Abdullahi Yusuf ya ce, wayon da gwamnonin ke nunawa wajen tsayar da magaji abu ne da  “bai wuci cikon cokali ba.”

Saboda a cewarsa, “Gwamnonin da ke ganin sun tsayar da wadanda suke so su gaje su  a tunaninsu za su damar ci gaba da gudanar da harkokinsu a jihohinsu wanda hakan babban kuskure ne.

“Wadanda kuwa suka kasa cimma matsaya daga gwamnonin sun shiga rudani, saboda mai yiwuwa sun yi wa wasu da dama alkawarin mika musu mulki shi ya sa har yanzu suka kasa ayyana mutum guda.

“Kamata ya yi a kyale ‘yan Najeriya zabi ‘yan takaran da suke ra’ayi, kodayake ina ji a raina cewa jam’iyyu masu tasowa za su ba da mamaki  muddin suka iy takunsu da kyau, saboda ‘yan Najeriya na neman sauyi,” inji Barista Yusuf.

Daga Ismail Mudashir (Abuja), Lami Sadiq (Kaduna), Hope A. Emmanuel (Makurdi), Abubakar Akote( Minna), Nabob Ogbonna (Abakaliki), Iniabasi Umo (Uyo), Victor Edozie (Port Harcourt), Aliyu M. Hamagam (Birnin Kebbi), Clement A. Oloyede (Kano), Eyo Charles (Calabar), Mohammed Abubakar (Dutse) Da Bashir Isah