2023: ’Yan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a sikeli
Daga cikin ’yan takarar Gwamnan, uku ne ake ganin za su fafata sosai a tsakaninsu.
Mulkin dimokuradiyya mulki ne da ake sa ran al’umma su zabi wanda suke so ya shugabance su, wa lau a matakin majalisun jihohi da tarayya ko mukaman gwamnoni da Shgaban Kasa.
Tuni jam’iyyun siyasa suka tsayar da ’yan takararsu, inda a Jihar Bauchi, jam’iyyu 15 suka fitar da ’yan takarar Gwamna.
Daga cikin ’yan takarar Gwamnan, uku ne ake ganin za su fafata sosai a tsakaninsu a karon battar shiga Gidan Gwamnatin Jihar a badi, wato wadanda suka fito daga jam’iyyun PDP APC da kuma NNPP.
Yayin da sauran ’yan takarar da suka fito daga jam’iyyun ZLP da APM da LP da SDP da PRP da ADC da ADP da AA da SDP da NRM da APP da YPP, manazarta harkokin siyasa na ganin ’yan rakiya ne kawai.
Sai dai Malam Ahmad Tijjani Kolo wani mai nazari da sharhi a kan harkokin siyasar Jihar Bauchi ya ce, ba a raina karfin dan takara, don haka sauran jam’iyyun na iya taka rawar gani a zabubbukan, musamman in aka lura da kururuwar da wasu ke yi cewa mutane sun gaji da jam’iyyun APC da PDP.
Iya Mashal Baba Sadik na APC
Jam’iyyar APC dai ta tsayar da tsohon Babban Hafan Sojin Sama Iya Mashal Sadik Baba Abubakar a matsayin dan rakararta.
An haifi Iya Mashal Sadik ne a garin Azare hedikwatar Karamar Hukumar Katagum da ke Jihar Bauchi.
Sojan sama ne da ya kai matsayin Babban Hafsan Sojin Sama na Kasa kafin ya yi ritaya.
A zantawa da manema labarai, Iya Mashal Sadik ya yi alkawarin dorawa a kan nasarorin da magabatansa suka yi, kuma ya nuna misalai da yake dogara da su cewa shi shugaba ne na kirki bisa irin ayyukan da ya gudanar a lokacin da yake aiki a matsayin sojin sama, inda ya samar da makarantu da asibitoci a Jihar Bauchi.
Mashal Baba Sadik ya ce, idan ya samu nasara zai tsaya ya nazarci matsalolin jihar, sannan ya warware su bisa aiwatar da bukatun da al’umma suka fi so ba abin da shi yake so ba.
Karfinsa
Ana ganin Iya Mashal Sadik zai samu goyon baya daga Gwamnatin Tarayya da kuma uwar Jam’iyyar APC ta Kasa.
Sannan ana zargin matarsa Hajiya Sadiyya Umar Farouk wadda ita ce Ministar Ayyukan Jin-kai za ta taimaka masa kwarai da gaske wajen karfafa samun nasararsa.
Haka kuma ana ganin Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu da tsohon Gwamnan Jihar, Malam Isa Yuguda da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara suna goyon bayan takararsa, wanda hakan babbar nasara ce gare shi.
Hakazalika, ana ganin Iya Mashal Baba Sadik yana da karfin aljihu da zai iya neman wannan kujera ba tare da wata fargaba ba.
Wasu na da ra’ayin cewa, tunda Iya Mashal Baba Sadik ya fito ne daga shiyya ta biyu mafi girma a jihar wato Bauchi ta Arewa, shiyyar da ta dade ba ta fitar da Gwamna ba tun 1983, suna ganin fitowar Sadik dama ce ga mutanen shiyyar ta mulki ya koma yankinsu.
Rauninsa
Jami’yyarsa ta APC tana fuskantar barazana sosai sakamakon ficewar wasu gwarazan ’ya’yanta wadanda suka koma PDP ko NNPP.
Daga cikin fitattun wadanda suka fice daga APC akwai Sanata Halliru Dauda Jika da Sanata Lawal Yahaya Gumau da Sanata Isa Hamma Misau da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Audu Sule Katagum da Alhaji Shitu Zaki da wanda ya nemi tsayawa takarar Gwamna a jam’iyyar, Alhaji Farouk Mustafa da sauransu.
Haka kuma, Sadik bai dade da shiga siyasa ba hasali ma daga barin sa aikin soja ne ya shiga takarar siyasa bayan ya rike mukamin Jakadan Najeriya a kasar Chadi, saboda haka masana siyasa suna ganin akwai wasu abubuwan siyasa da ba zai sani ba.
Sannan ga babban kalubalen da ke gabansa na hado kan ’ya’yan jam’iyyar da suka rage, musamman wadanda suka yi takara suka fadi a zaben fidda-gwani na jam’iyyar da kuma yadda zai rike manyan ’yan siyasa irin su Yakubu Dogara wanda ake gani suna da sabani da uwar jam’iyyar ta kasa saboda gaza daukar mataimakin dan takarar Shugaban Kasa daga mabiya addinin Kirista.
Halliru Dauda Jika na ANPP
Shi ne mafi karancin shekaru a tsakanin ’yan takara mafiya karfi kuma shi ne Sanatan Bauchi ta Tsakiya.
Karfinsa
Halliru Jika ya kwana biyu yana siyasa, inda ya taba zama Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, kuma ya yi dan Majalisar Wakilai daga mazabar Darazo da Ganjuwa sau biyu kafin ya zama Sanata.
Jika ya fice daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP ne bayan ya sha kaye a zaben fid-da-gwani, inda aka ba shi takarar Gwamna a zaben 2023, Jika dan siyasa ne da aka san kamun ludayinsa.
Ya samu nasara a duk takarar siyasar da ya yi, kuma gogewarsa a fagen siyasa ta sa ya kasance Shugaban Kwamitin Harkokin ’Yan sanda a Majalisar Wakilai da kuma Majalisar Dattawa.
Shi ma yana da karfin aljihu da zai iya neman kujerar Gwamna kuma jam’iyyarsa ta NNPP a zaben 2019 ta lashe kujerar dan Majalisar Wakilai na Birnin Bauchi, sannan akwai ’yan siyasa masu karfi da suka koma jam’iyyar kamar Sanata Isa Hamma da Sanata Lawal Yahaya Gumau ga kuma farin jinin jagorar Jam’iyyar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da ake ganin zai yi tasiri wajen samun nasararsa.
Rauninsa
Sai dai wasu kwararrun ’yan siyasa suna ganin Halliru Jika ba zai yi wata rawar gani ba a zaben Gwamnan, saboda suna ganin jam’iyyarsa ba ta da karfi kamar PDP da APC a dukkan kananan hukumomi 20 da ke jihar.
Sannan Halliru Jika ya fi karfi ne kawai a Shiyyar Bauchi ta Tsakiya, amma a sauran shiyyoyin sai ya zage damtse.
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na PDP
Sanata Bala Muhammad Abdulkadir shi ne Gwamna mai ci kuma dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP don sake dawowa a karo na biyu.
Karfinsa
Sanata Bala Mohammed ya dade a fagen siyasa, inda ya zama Sanatan Bauchi ta Kudu kafin ya zama Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ana ganin Gwamna Bala zai yi amfani da karfin madafun iko da ke hannunsa don ganin ya koma kan kujerarsa a 2023.
Sannan akwai masu ganin ayyukan raya kasa da ya yi a asassan jihar za su sa al’umma su sake zaben sa.
Gwamnan ma yana da karfin aljihu kuma kasancewar jam’iyyarsa ta PDP ta kafu sosai a jihar, hakan zai taimaka masa wajen samun nasara.
Wani abu da ake ganin zai taimaka masa shi ne matakin sasantawa da dukkan ’yan takarar da suka shiga zaben fidda-gwani, wadanda ake ganin idan ya shawo kansu zai samu karin goyon bayan da zai kai shi ga nasara.
Rauninsa
Babbar matsalar da Gwamnan yake fuskanta ita ce, zai yi wuya wadanda suka zabe shi a 2019 su sake zabar sa, idan aka yi la’akari da kuri’u kadan ya hau kujerar.
Yanzu dai ya bata da wasu da suka taimake shi a wancan karo kamar tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da Sanata Isa Hamma da Alhaji Mahmud Maijama’a da sauransu.
Wasu daga cikinsu tuni sun koma wasu jam’iyyu.
Haka kuma, Gwamnan zai fuskanci matsala daga ma’aikata saboda yadda gwamnatinsa ta shafe sama da shekara uku tana wahalar da su kan batun biyan albashi.
Ga matsalar kudin hutu da rashin biyan garatuti. Akwai masu cewa duk da ya gaji matsalolin ne, amma ya kasa magance matsalar alhali hakan na cikin abubuwan da ya yi yakin neman zabe a shekarar 2019.
Sannan akwai matsalar rashin isassun ma’aikata a fannonin kiwon lafiya da ilimi.
Sai korafin da jama’a ke a kan waziran da yake da su, wadanda suke taka kafafun masu zabe, kuma ba su yi wa al’ummarsu abin da ya kamata ba.
Wani mai fashin baki kan harkokin siyasa, Alhaji Muhammad Jibril Sogiji ya ce, idan aka duba tarihin Jihar Bauchi tun daga marigayi Gwamna Tatari Ali, babu Gwamnan da ya koma a karo na biyu cikin sauki, saboda cin zaben Gwamna karo na biyu a Bauchi ba karamin yaki ba ne.
Ya ce, lokacin Gwamna Ahmad Mu’azu da Gwamna Isa Yuguda kowanensu ya sha wahalar komawa karo na biyu, wahalar da ta fi wadda suka sha a karon farko.
Sannan ga tsohon Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar da ya gaza komawa a karo na biyu duk da irin yakin neman zaben da ya yi.
Alhaji Jibril Sogiji ya ce, a siyasar Jihar Bauchi babu wanda zai yi bugar kirji ya ce zai iya kawo wuri guda.
Ya kara da cewa, lamarin zaben Gwamna a Bauchi babu mai bugun kirji ya ce wane ne zai kai labari, don haka za a fafata sosai a zaben 2023.