2023: Zulum zai fito takarar shugaban kasa

Rushe majalisar zartarwa da Zulum ya yi zai ba kwamishinoni damar fitowa takarar Gwamnan Bonro.

2023: Zulum zai fito takarar shugaban kasa

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum

Jama’a, a gafarce ni idan abin da na rubuta a wannan makala bai tabbata ba. 

Haka kuma, ina rokon Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, wanda na yi wannan rubutu a kansa, ya yi min afuwa, idan hasashena kan irin guguwar da ta taso a siyasar Najeriya ya kasance da kuskure.

Wannan lissafi ne irin nawa, idan ka hada daya da daya za su zama biyu, amma ban yi magana da shi ba, ko wani dan siyasa game da batun shugabancin Najeriya a 2023.

Madogarata a wannan lamari ita ce idanuwa irin na mai lura da kuma kunnuwan mai sauraro da kunnen basira.

Ku dai biyo ni:

Ranar Alhamis Farfesa Zulum ya rusa majalisar zartarwarsa, wanda bakon abu ne ga mutum kaifi daya wanda yake la’akari da cancanta fiye da bukatun siyasa wajen yin nade-nade.

Shin ko dai akwai wani abu ne da ya taso na gaggawa? Ruwa ba ya tsami banza.

Jam’iyyar Zulum ta APC mai mulki tana wasan wa-ta-gangano da babbar jam’iyyar adawa ta PDP kan batun yankin da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 zai fito.

Yanzu kusan shekara ke nan da abokinmu, Farouk Adamu Aliyu, wanda na hannun daman shugaban kasa ne, ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa zabinsu na dan takarar shugaban kasa ya ta’allaka ne da zabin PDP.

Abin nufi shi ne, idan PDP ta bai wa dan Arewa tikitin, to APC ba ta da zabi illa ta bi sahu, kasancewar yankin Arewa ke da mafi yawan kuri — Har yanzu da wannan lissafi ake amfani a siyasar Najeriya.

A makon jiya, Shugaban APC na Kasa ya yi irin wannan furucin, inda ya ce duk mai sha’awa zai iya neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Amma fa ba bisa radin kanta APC ta yi hakan ba; hasali ma ta furta kalamai marasa dadi game da yiwuwar bai wa dan Arewa takara a PDP.

A wata hira da jaridar Punch ta wallafa a wannan makon, daya daga cikin mutanen da suka yanke wa APC cibiya, Osita Okechukwu, a fusace ya zargi PDP da wuruwuru da kuma tilasta wa APC sauya lissafi.

A cewar Mista Okechukwu: “PDP na so ta karbi mulki ko ta halin kaka, ciki har da ta hanyar wuruwuru.

“Mun san PDP ta yankwane ta susuce don haka take neman shugabancin kasa a 2023 ido rufe.

“PDP ta san cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba zai sake tsayawa takara ba a 2023 don haka suke ganin za a samu wani gibi da za su cike.

“Tabbas sun yi tunanin cewa za su iya lashe kuri’un da Buhari ke samu idan har suka bai wa dan Arewa takara.

“Lissafin da PDP ke yi ba ji ba gani cike yake da son zuciya ta yadda har suka yi karan tsaye ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma cin fuskar magoya bayanta na shekara da shekaru kuma ’yan ga-ni-kashe-ninta na yankin Kudu, musamman Kudu maso Gabas”.

Ni dai na rasa gane wanda idonsa ya rufe wajen neman mulki ko ana ha maza, ha mata tsakanin APC da PDP.

Idan ba haka ba, ai kamata ya yi Mista Okechukwu da APC su saba wa PDP su yi abin da ya dace ta hanyar tsayawa su bai wa yankin Kudu takara.

Amma idan APC ta kwaikwayi kuskuren da PDP ke shirin yi, ta juya wa Kudu baya, ta bai wa dan Arewa takara, to ai dukkansu sun zama shegiyar darin.

Kuma, idan har da gaske Shugaba Buhari yana da kuri’a miliyan 12 da APC take riyawa, to me zai hana ta kwantar da hankalinta ta sa ya kawo mata wadannan tulin kuri’un da take ikirari?

Gaskiyar magana ita ce ’yan siyasa masu hangen nesa irin su Shugaban Jam’iyyar ta APC, Sanata Abdullahi Adamu, sun san cewa wadannan kuri’un sun watse.

Shekara bakwai na shugabancin Buhari sun zaizaye su ta yadda a yanzu babu dan takara da za ka samu a Arewa – tun daga dan takarar kansila har na shugabancin kasa – da ke hada hotonsa da na Buhari a fastar kamfe dinsa.

Mutane irin su Sanata Abdullahi Adamu sun san cewa, “Babu abin da ya fi rasa mulki tashin hankali in banda na Tashin Kiyama” kamar yadda wani shugaban reshen Jihar Bauchi na PDP ya bayyana a 2020.

Shi ma Shugaban na APC tsohon gwamna ne a karkashin PDP, don haka ba zai yaudari kansa ba.

Da ya bai wa dan Kudu takara — bayan Gwamnatin Buhari ta APC ta bai wa ’yan Arewa kunya – daga karshe dan takarar da PDP ta tsayar daga Arewa ya kayar da su, gwamma ya yi watsi da tsarin karba-karba ya ceto APC da ’ya’yanta daga tashin Kiyamar Duniya da wancan dan siyasar ke magana.

Yana sane da cewa yanzu ’yan Arewa ba su da kwarin gwiwar da za su saki jiki da shugaban kasa dan Kudu. Sam ba su da nutsuwa da karba-karba kamar yadda suka yi a 1999.

A wajen zaben dan takararta daga Arewa kuma, muna sa rai jam’iyyar APC a karkashin Abdullahi Adamu za ta shafa wa idonta toka ta yi amfani da takobi gaya-wa-jini-na-wuce.

Ya kwana da sanin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, da Gwamna Bala Mohammed, da Gwamna Aminu Tambuwal, da Bukola Saraki, za su daka wasoso a kan “taskar kuri’a miliyan 12”, don haka tsayar da dan takarar da bai kai su ba a APC daidai yake da busa wa jam’iyyar kaho a 2023.

Saboda haka ne a Arewar babu tantama APC za ta so zabo dan takara mai farin jini ga jama’a ba kawai wanda ya fito shiyya daya da su Atiku ba.

Irin dan takarar da APC ke bukata

Ko ba komai, babu wanda zai nuna wa Turakin Adamawa ko Kauran Bauchi ko Mutawallen Sakkwato Arewa.

Ke nan APC na bukatar mutumin da dan asalin Arewa ne hakika, sannan take da tabbacin zai iya lashe mata kuri’un ’yan Arewa kamar yadda take da tabbacin rana za ta fito gobe da safe.

Tana bukatar mutumin da yake da halayen da ’yan Arewa suke matukar sha’awa da suka hada da yin tsayin daka wajen kwato hakkin talaka da jajircewa wajen tabbatar da adalci, da kuma – a yanzu bayan abin da aka gani a mulkin Buhari – katafila sarkin aiki wanda ba zai sarayar da muradun Arewa don wata shiyya ba sannan ya shawo kan matsalar tsaro da rashin cigaban da yankin ke fama da su.

A takaice tana bukatar dan takara wanda da zarar an ce “kule” bayan zaben fitar da gwani, zai casa dan takarar PDP ta yadda tun kafin ma a yi zaben zai runtuma shi da kasa.

Wannan lissafin ne ya shigo da Farfesa Zulum cikin raskwanar da APC ke yi a kan kujerar shugaban kasa a 2023.

Babu wani dan takara a Arewa da zai iya biya wa jam’iyyar wannan bukata sama da shi.

A fadin Arewa ana yi mishi kallon mutum mai gaskiya, jarumi, jajirtacce, mai kwazo, mai saukin kai, wanda ba ya daukar shirme, ga shi kuma mai tausayi.

Shi ne wanda ya tattara siffofin da a tunanin mutanen Arewa ya kamata shugaba ya kasance yana da su.

Sannan, a lisafin kura-ta-ci-kura na APC, ya kasance shagon da zai yi wa dan takarar PDP dukan kawo wuka kafin kiftawa da Bismilla.

’Yan Arewa kalilan ne za su yi kasadar saba wa hakan.

Shin PDP na da irin Zulum?

Ba na tantama cewa a PDP akwai ’yan takarar da za su iya taka rawar gani kamar Zulum, amma, kamar yadda ake cewa, siyasa na bukatar farin jini, kuma a yanzu  dai, tauraruwar Zulum ce take haskawa.

Bugu da kari, ga alfarmar mulki da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Fadar Shugaban Kasa da sauran cibiyoyin gwamnati.

Saboda haka ne Zulum ya tsinci kansa a cikin jerin mutanen da suka mulki Najeriya ba tare da sun yi niyya ba — irin su Tafawa Balewa, da Obasanjo a 1976, da Shagari, da Buhari a 1984, da Obasanjo a 1999, da Yar’Adua da Jonathan.

Har zuwa lokacin da nake rubuta wannan makala dai Zulum bai sayi fom ba, amma hakan ba ya nufin cewa babu wata tattaunawar bayan fage a tsakaninsa da jam’iyyar.

Amma dai zuwa ranar Alhamis lokaci yana kurewa — a tunanina wannan shi ne dalilin rusa majalisar zartarwarsa.

Idan hasashenmu game da wannan yanayi na kar-ta-kwana ya tabbata, to dole Zulum ya yi gaggawar rushe majalisar saboda APC ba ta da wani dan takarar gwamna a Jihar Borno a halin da ake ciki.

INEC kuma ta tsaya kai da fata a kan wa’adin da ta bai wa jam’iyyu na 6 ga watan Yuni da su mika sunayen ’yan takararsu.

Don haka ketare 6 ga watan Mayu na nufin idan Zulum zai tsaya takarar shugaban kasa – kuma mutane da dama sun yi amanna jam’iyyarsa za ta jawo shi ya fito a karshen lokaci – to babu wanda zai yi takarar gwamna a cikin kwamishinoninsa domin kuwa ba za su cika sharadin ajiye mukamin siyasa wata guda kafin zaben fitar da dan takara ba.

Wannan ne ya sa ina jin labarin cewa ya rushe majalisar zartarwar Jihar Borno, na kara samun babban tabbacin karshe na hasashena kan abin da zai iya faruwa, ko da yake ina can kilomita 500 daga Maiduguri.

Idan ba haka ba, ba dabi’ar dogon farfesan mai magana daya ba ne ya rushe majalisar zartarwarsa a irin wannan lokaci a cikin wa’adin mulkinsa.

Hakan da ya yi zai bai wa kwamishinoninsa, da ma duk wani dan APC mai sha’awa a Jihar Borno, damar tsaywa takarar gwamnan jihar.

A dakaci Zulum.

 

Dokta Aliyu Tilde ya rubuto wannan makala ne daga Bauchi; Bashir Isah ya fassara.

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira