2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Wannan shi ne karo na 13 da wutar lantarkin ta lalace cikin watanni 13 da suka gabata.

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Najeriya ta sake tsunduma cikin duhu bayan faɗuwar babban layin samar da wutar lantarki na ƙasa, da yammacin ranar Asabar.

Wannan ɗaukewa ita ce karo na farko a shekarar 2025, amma karo na 13 cikin watanni 13 da suka gabata.

Rahotanni sun nuna cewa wutar lantarki ta fara raguwa daga megawat 2,111.01 da misalin ƙarfe 2 na rana.

Daga bisani ta sauka zuwa megawat 390.20 da misalin ƙarfe 3 na rana.

A shekarar da ta gabata, layin samar da wutar lantarkin ya lalace sau 12, wanda hakan ya jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin duhu tare da kawo cikas ga tattalin arziƙi da rayuwar yau da kullum.

Wannan lalacewar na zuwa ne kwanaki 11 kacal da shiga sabuwar shekarar 2025.

Hakan ya sake nuna yadda matsalar rashin ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki ke ta’azzara a ƙasar.

Al’ummar Najeriya dai na ci gaba da fuskantar ƙalubale a fannin samar da wutar lantarki, wanda ke da matuƙar tasiri a harkokin kasuwanci, masana’antu, da rayuwar yau da kullum.

Wannan yana ƙara jaddada buƙatar gaggawar gyara tsarin samar da wuta a ƙasar.

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani