2027: Kotu ta ayyana ranar yanke hukunci a shari’ar neman cancantar takarar Jonathan

Cikin ƙarar da aka shigara ana neman kotu ta hana Jonathan tsayawa takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 a kowacce jam’iyya.

2027: Kotu ta ayyana ranar yanke hukunci a shari’ar neman cancantar takarar Jonathan

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta ayyana 26 ga watan Mayun bana a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a ƙarar da ke neman cancantar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027.’

Mai shari’a Peter Lifu ne ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar yanke hukunci bayan sauraron hujjojin lauyoyin mai ƙara da kuma waɗanda ake ƙara.

Aminiya ta ruwaito cewa, wani mutum mai suna Jideobi ne ya shigar da ƙarar yana neman kotu ta hana Jonathan tsayawa takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 a ƙarƙashin kowacce jam’iyya.

Mai ƙarar ya kuma roƙi kotun da ta hana Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC karɓa ko tantance sunan Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

A ƙunshin ƙarar da ya shigar, ya nemi kotun da ta warware tufkar da ke cikin tanade-tanaden sashe na 1(1), (2), (3) da kuma 137(3) na Kundin Tsarin Mulkin 1999, wadda ka iya halasta ko haramta wa Jonathan cancantar sake neman kujerar shugaban ƙasa.