2027: Kwankwaso da Aregbesola sun gana kan makomar siyasar Najeriya

Ganawar dai ba za ta rasa nasaba da yunƙurin da wasu ke yi na haɗa kan ’yan adawa domin tunkarar babban zaben 2027.

2027: Kwankwaso da Aregbesola sun gana kan makomar siyasar Najeriya

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas.

Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya.

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke kira ga haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027.

A watan Oktoban 2024, jam’iyyar APC a Jihar Osun ya dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam’iyya da sukar shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande.

Aregbesola, wanda ya kasance gwamnan Osun daga 2010 zuwa 2018, ya fuskanci rikici da magajinsa, Adegboyega Oyetola, tun bayan zaɓen 2018.

Wannan rikici ya haifar da rabuwar kai a cikin jam’iyyar APC a Osun, inda wasu magoya bayan Aregbesola suka kafa ƙungiyar Omoluabi Progressives, wanda jam’iyyar ta yi zargin cewa tana aiki ne a matsayin waniɓangare mai adawa da ita.

Duk da waɗannan ƙalubale, Aregbesola ya ci gaba da kasancewa mai faɗa a ji a siyasar Najeriya.

Ganawarsa da Kwankwaso na iya nuna yunƙurin ƙulla sabbin alaƙa da haɗin gwiwa tsakanin shugabannin siyasar domin inganta dimokuradiyya a Najeriya.

Har zuwa yanzu, ba a samu cikakken bayani kan abin da suka tattauna ba, amma ganawar ba za ta rasa nasaba da yunƙurin da wasu ke yi na haɗa kan ’yan adawa domin tunkarar babban zaben 2027.

Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa

Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri

Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa

Sojoji sun tarwatsa maɓoyar Bello Turji a Zamfara