2027: Lissafin siyasa ya sauya bayan Obi da Kwankwaso suka koma NDC
Majiyoyi sun ce Obi da Kwankwaso ba su gamsu da yadda ake tafiyar da jam’iyyar ba, gami da yadda ake kallon ta a matsayin mallakar wani bangare
Tafiyar siyasar zaben shekarar 2027 ta dauki sabon salo bayan tsohon dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, da na NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun sauya sheƙa daga Jam’iyyar ADC zuwa Jam’iyyar NDC.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin biyu sun gana da jagoran jam’iyyar, tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson, a Abuja ranar Lahadi, inda bayan tattaunawa aka ba su katin zama ’ya’yan jam’iyyar.
Sauya sheƙar tasu na zuwa ne bayan rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar ADC, musamman kan batun shugabanci da kuma rashin fayyace tsarin karba-karba da kuma yankin da za ta ba wa takarar shugaban ƙasa a zaben na 2027.
Majiyoyi sun ce Obi da Kwankwaso ba su gamsu da yadda ake tafiyar da jam’iyyar ba, gami da yadda ake kallon ta a matsayin mallakar wani bangare, da kuma rashin bayyana matsaya kan yankin da za a ba wa tikitin shugaban ƙasa.
- ’Yan bindiga sun sa wa mamona harajin N10m a Katsina
- Pantami zai je kotu bayan APC ta ba Jamilu Gwamna takarar Gwamnan Gombe
Haka kuma, ci gaba da shari’o’in kan rikicin cikin gida ya kara dagula al’amura, lamarin da ya sa suka fara neman wata sabuwar mafita.
An ce sun zabi Jam’iyyar NDC ne saboda kasancewarta sabuwar jam’iyya wadda ba ta fuskantar irin rikice-rikicen da suka bari a ADC baya.
Masana siyasa na ganin cewa wannan mataki na iya kawo sauyi mai girma a siyasar adawa, musamman ganin karfin magoya bayan da shugabannin biyu ke da shi a fadin ƙasa.
Sai dai wasu jam’iyyun siyasa sun soki matakin, suna zargin cewa sauya sheƙar na da nasaba da neman tikitin shugaban ƙasa cikin sauki.
Haka kuma, ana ganin wannan sauyi na iya kawo cikas ga kokarin hada kan jam’iyyun adawa domin fitar da dan takara guda a zaben 2027.