2027: Neman tazarce ba ya gabana yanzu — Tinubu

Ina so Nijeriya ta samu ci gaban da hatta waɗanda ba a haifa ba su ma za su ci moriya.

2027: Neman tazarce ba ya gabana yanzu — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya jaddada ƙudirinsa na kawo ingantaccen sauyi domin bunƙasa yalwar arziki mai ɗorewa a Nijeriya.

Saboda haka Tinubu wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar da ta gabata, ya ce a yanzu neman tazarce ko batun neman wa’adi na biyu a Zaɓen 2027 ba shi ne a gabansa ba.

A cewar Shugaba Tinubu, hankalinsa ya karkata ne kan yadda Nijeriya za ta samu ci gaban da hatta waɗanda ba a haifa ba za su ci moriya.

Tinubu wanda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ya wakilta, na wannan furuci ne a yayin wani taro da jam’iyyar APC reshen Kudu maso Yamma ta gudanar a Otel ɗin Eko da ke Victoria Island a Jihar Legas.

A yayin taron wanda Gwamnan Legas Mista Babajide Sanwo-Olu ya kasance mai masaukin baƙi, Tinubu ya ce yana jin raɗaɗin dangane da ƙunci da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar, yana mai jaddada cewa daɗi na tafe nan ba da jimawa ba.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon Gwamnan Ekiti, Dokta Kayode Fayemi da takwarorinsa na Jihar Ogun — Ibikunle Amosun da Cif Olusegun Osoba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito sauran mahalarta sun haɗa gwamnonin Ekiti, Ondo da Ogun.

Kazalika, sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da sauran ƙusoshin gwamnati daga jam’iyyar APC sun albarkaci taron.

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025

Za a rataye shi saboda kisan jariri