2027: Tinubu zai samu gagarumar nasara a Kano — Gwamna Abba
Gwamnan ya ce za su yi aiki tuƙuru domin tabbatar da nasarar Tinubu a jihar.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027 a jihar.
Ya ce Kano za ta bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC ƙuri’u masu yawa.
- Mahara sun kashe manoma 6 a kauyen Malumfashi
- An kama kwamandojin Boko Haram 7 a Katsina bayan sun dawo aikin Hajji
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da zaɓaɓɓun jami’an gwamnati da waɗanda aka naɗa a Fadar Gwamnatin Kano.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Abba ya ce ba ya nadamar goyon bayan Shugaba Tinubu, yana mai cewa sake zaɓensa aiki ne da ya rataya a wuyan dukkanin mambobin APC da jami’an gwamnati.
Ya umarci dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da ba su yi rajista a APC ba da su yi cikin gaggawa.
Ya ce dole ne duk wani jami’in gwamnati da aka zaɓa ko aka naɗa ya kasance cikakken ɗan jam’iyyar tare da taka rawa wajen ƙara mata ƙarfi kafin zaɓen 2027.
Gwamna Abba, ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi aiki domin APC ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Majalisar Dokokin Jiha da kuma na Ƙananan Hukumomi.
Gwamnan ya raba wa hadiminsa sama da 300 filaye.
Haka kuma ya amince a bai wa kowane daga cikinsu tallafin kuɗi Naira 100,000.
Da yake jawabi a taron, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Ismail Falgore, ya ce APC za ta ci gaba da bayyana ayyukan alherin da Shugaba Tinubu ke yi a Kano.
Ya ƙara da cewa ayyukan mazaɓu da ’yan majalisar suka gudanar tare da goyon bayan gwamnan su ƙara wa jam’iyyar karɓuwa a faɗin jihar.
Shi ma Shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya ce jam’iyyar ta shirya tsaf domin tunkarar zaɓen 2027.
Jami’an gwamnati sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaba Tinubu da Gwamna Abba, tare da alƙawarin ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a domin APC ta samu nasara a zaɓen 2027.