22,40,Allah Ya yi wa Sarkin Nufawan Benin rasuwa

Allah ya yi wa Alhaji Idiris Sani Sarkin Nufawa Benin Rasuwa a cikin wannan makon a ranar Litini da ta gabata. Sarkin rasu ne bayan fama da jinya na tsawon lokaci. Ya rasu ne yana da shekaru 73 a duniya, ya kuma bar matan aure uku da ‘ya’ya da jikoki da dama. Takwaran aikinsa Sarkin […]

22,40,Allah Ya yi wa Sarkin Nufawan Benin rasuwa
22,40,Allah Ya yi wa Sarkin Nufawan Benin rasuwa

Allah ya yi wa Alhaji Idiris Sani Sarkin Nufawa Benin Rasuwa a cikin wannan makon a ranar Litini da ta gabata. Sarkin rasu ne bayan fama da jinya na tsawon lokaci. Ya rasu ne yana da shekaru 73 a duniya, ya kuma bar matan aure uku da ‘ya’ya da jikoki da dama.

Takwaran aikinsa Sarkin Hausa Benin Alhaji Isah Adamu ya bayyana irin kyawawar halayyar marigayin da cewa, mutum ne da ke da nutsuwa a harkar shugabancin jama’a ciki da waje.
‘’Ni dai abin da na sani game da halayyar marigayi Sarkin Nufawa, wanda zan iya bayyana a ciki na farko duk wanda ya san marigayin ya san shi da halin dattaku, kuma mai hakuri da kula da sha’anin shugabanci bashi da ha’inci ko zalunci, tun daga lokacin da na san shi kawo lokacin da Allah ya yi masa rasuwa, ban taba jin yana takun saka da wani ba, har ya bar duniya. Don haka babu abin da na iya da ikon Allah, sai dai addu’a Allah ya gafarta masa, ya sanya shi cikin rahama,” inji shi.
Kuma tuni an yi suturarsa a garin Bida kamar yadda Musulunci ya tsara. Allah Ya jikansa da rahama, kuma ya bai wa iyalansa da sauran ‘yan uwa hakuri game da wannan babban rashin da aka yi.