Jirgin Air Peace ya yi saukar gaggawa a Legas

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da jirgin ya taso daga birnin Fatakwal zuwa Legas.

Jirgin Air Peace ya yi saukar gaggawa a Legas

Wani jirgin saman kamfanin Air Peace ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da jirgin ya taso daga birnin Fatakwal zuwa Legas.

“Muna sanar da al’umma lamarin da ya faru da jirginmu da ya taso daga birnin Fatakwal zuwa Legas ranar 25 ga watan Afrilu.

“Mintuna kafin saukar, sai matuƙin jirgin ya fahimci wata alamar ƙarar gargaɗin wuta a inda direban ke zama.

“Direban ya yi ƙoƙarin ɗaukar duka matakan kariya, kodayake daga baya ƙarar ta daina.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “Direban ya yi gaggawar sanar da masu kula da filin jirgin na Legas, inda bayan saukar jirgin aka gano cewa ƙarar ta fara kaɗawa ne bisa kuskure, amma babu wata wuta da kama a jirgin.

Bayanai sun ce jirgin wanda ke ɗauke da fasinjoji 243 tare da ma’aikatan jirgin 12, ya sauka lafiya ba tare da wata matsala ba.

Lamarin dai na zuwe ne kwanaki bayan jirgin kamfanin Dana Air ya zame daga kan hanyarsa a filin jirgin saman na Legas, dalili ke nan da gwamnatin ƙasar da dakatar da kamfanin daga aiki, tare da ƙaddamar da bincike kan batun.

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025