Za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi a Yobe — Jam’iyyun adawa
Mun shirya tsaf domin shiga wannan zabe amma kuma muna sara ne muna duba bakin gatarinmu.
A yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomin a ranar Asabar ta karshen wannan wata na Mayu a Jihar Yobe, wasu shugabannin jam’iyyun adawa da ke jihar da suka hada da Jam’iyyar NNPP da PDP da AD da PDM sun bayyana shirinsu na shiga wannan zabe matukar za a ba su damar shiga takarar ba tare da an yi musu kwange ba.
Shugaban Jam’iyyar NNPP a Jihar Yobe, Alhaji Yakubu Shehu Damagum ya bayyana wa Aminiya cewa, jam’iyyarsu ta NNPP a Jihar Yobe ta shirya tsaf don shiga zaben kananan hukumomin matukar Hukumar Zabe ta Jihar Yobe ta amince ta sayar musu da fom din tsayawa takarda.
Shugaban ya ce, Jam’iyyar NNPP ba ta wata tantama a kan shiga zaben, kamar yadda wasu ke cewa jam’iyyun adawa a jihar ba za su shiga zaben ba, inda ya fito karara ya karyata wannan magana.
Ya kara da cewar, babban abin da ke gabansu shi ne samun fom din tsayawa takarar daga Hukumar Zaben jihar da kuma samun ainihin ’yan takarar da ke da sha’awar tsayawa takarar.
Ya bayyana cewa domin kuwa ya zuwa yanzun dan takara daya tak suka samu na kansila daga Karamar Hukumar Karasuwa, wanda shi kadai ne ya zuwa yanzu ya fito ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a duk Jihar Yobe, amma ba su san nan gaba.
Shugaban na NNPP ya kara da cewar, tuni Jam’iyyarsu ta NNPP ta tura takardarsu zuwa Hukumar Zabe ta Jihar Yobe domin bayyana shirinsu na shiga zaben.
Shi ma Shugaban Jam’iyyar AD, Malam Habu Doro Potiskum bayyana wa Aminiya matsayarsu a kan cewa, su ma a shirye suke su shiga cikin wannan zabe na kananan hukumomi a Jihar ta Yobe, amma kuma suna sara ne suna duba bakin gatarinsu, domin ba zai yiwu a ba su ga ana aikata ba daidai ba kuma su zuba ido, kasancewar akwai amanar al’umma a kansu.
Ya ce, suna sane da cewar kai da kaya duk mallakar wuya ne, ma’ana da Hukumar Zaben jihar da ma’aikatanta duk mallakin Gwamnatin Jihar Yobe ne, inda ba za su taba yarda ’yan takararsu a kowane mataki su fadi zabe ba, wanda hakan ke nuna cewar, in jam’iyyun adawa suka shiga ma, sun san yadda sakamakon zaben zai kasance.
Game da ko jam’iyyarsu tana da ’yan takara, sai shugaban ya bayyana cewa, zuwa yanzu ba su da dan takara ko da guda, wanda a ganinsa hakan ba ya rasa nasaba da tunanin da jama’a ke yi cewar, idan mutum ya fito ma bata lokacinsa da kudinsa kawai zai yi.
Ya ce kasancewarsu ’yan jam’iyyar adawa suna ganin cewa duk wanda ya fito takara ba lallai ba ne ya ci zaben, komai kuwa yawan jama’arsa, domin kuwa Hukumar Zabe ta jihar ita za ta shirya zaben kamar yadda kowace jiha ke yi.
A tattaunawar Aminiya kuwa da Shugaban Jam’iyyar PDM a Jihar ta Yobe dangane da yiwuwar shigar jam’iyyar zaben ya ce, zuwa yanzu dai kam ba su yanke shawarar komai ba a kan yiwuwar shiga zaben ko kuma akasin hakan, amma za su sanar da matsayarsu nan gaba kadan.
A nasa bangaren, Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Sanata Umar El-Gash ya ce, shakka babu jam’iyyarsu za ta shiga zaben kuma za a fafata da ita, fata dai kawai shi ne a yi adalci.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don shugaban ya yi mata karin haske a kan irin shirn da jam’iyyar ta yi game da shiga zaben ya ci tura, domin kuwa yana cikin yi wa wakilinmu bayani ta waya, sai ta katse.
A bangaren Hukumar Zabe ta Jihar Yobe kuwa, wanda hakkinta ne shirya zaben, ita Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin shugaban, Dakta Mamman Mohammad game da shirin da suke yi a kan zaben, amma ya ci tura.