Gwamnatin Kano za ta fara ɗaukar nauyin shirya fina-finan Kurame

Matakin wani yunkuri ne na rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Gwamnatin Kano za ta fara ɗaukar nauyin shirya fina-finan Kurame

Gwamnatin Kano za ta fara ɗaukar nauyin shirya wasannin dabe da fina-finan masu larurar ji a jihar.

Gwamnatin karkashin Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta ce matakin ya biyo bayan yunkurinta na rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Yayin ganawarsa da kungiyar masu wasan dabe da fina-finan kurame na Kano, Shugaban Hukumar Abba Almustapha, ya ce baya ga samar da aikin yi, fina-finan za su taimaka wajen nishadantarwa, da kuma ilmantar da masu larurar ji da ke jihar.

Almustapha, ya kuma ja hankalin kungiyar da ta yi rajista da hukumar domin fara cin gajiyar dukkanin shirye-shirye da tallafin gwamnati, domin fara shirya wasanni masu ingancin da za su samar musu da masu kallo a duniya baki ɗaya.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar, Malam Rabiu Aliyu Adamu ya bayyana farin cikinsa da kyakkyawar tarbar da suka samu daga Almustaphan, da kuma shawarwarin da ya ba su, tare da alkawarin dabbaka su nan ba da jimawa ba.