A Yi Amfani Da Halayen Sardauna Wajen Magance Matsalolin Arewa —Kungiyar Inganta Cigaban Arewa

Kungiyar Inganta Cigaban Arewa da aka fi sani da suna Rebuild Arewa Initiatibe 4 Debelopment (RAID), ta yi kira ga masu rike da madafun iko da sarakunan Arewacin Nijeriya da Dattawan Arewa da su yi koyi da halayen marigayi Firimiyan Arewa Sir, Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato don shawo kan matsalolin da suka yi wa yankin […]

A Yi Amfani Da Halayen Sardauna Wajen Magance Matsalolin Arewa —Kungiyar Inganta Cigaban Arewa

Kungiyar Inganta Cigaban Arewa da aka fi sani da suna Rebuild Arewa Initiatibe 4 Debelopment (RAID), ta yi kira ga masu rike da madafun iko da sarakunan Arewacin Nijeriya da Dattawan Arewa da su yi koyi da halayen marigayi Firimiyan Arewa Sir, Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato don shawo kan matsalolin da suka yi wa yankin na Arewacin Nijeriya dabaibayi.

Kungiyar fadi haka ne ta bakin Daraktan Tsare-tsare da Yada Labaranta Kwamared Bitako Abubakar Umar wanda ya bayyana haka a wani taro da kungiyar ta yi da manema labarai a jiya Juma’ a Abuja, inda ta bayyana cewa, halayen Sardauna na gaskiya da rikon amana da tallafar kowa ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba, su suka sanya Yankin Arewa ya ci gaba kuma ya zama tsintsiya madaurinki daya a zamanin mulkinsa.

Kwamared Bitako, ya kara da cewa, “matsalolin tsaro na ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da fadace-fadacen kabilanci da tabarbarewar ilimi da kuma kangin talauci da suka addabi Arewa duk sun sami gindin zama ne saboda rashin adalcin shugabannin da suke tafiyar da al’amurran Arewa a yau.”

Kungiyar ta kuma yi tir da yadda a yanzu ake son a manta da gudumawar da Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da kuma Firaministan Nijeriya marigayi Sir, Abubakar Tafawa Balewa suka bayar ta hanyar kasa raya ranar da suka rasa rayukansu da ayyuka na tunawa da su.

“Marigayi Firimiyan Arewa Alhaji Sir, Ahmadu Bello da marigayi Firaministan Nijeriya Alhaji Sir, Abubakar Tafawa Balewa sun bayar da gudumawar duk wani abu da suke da shi, ciki har da rayukansu don cigaban Arewa.

Sun rasa rayuwarsu a kokarinsu na kafa harsashen tubalin cigaban al’ummar Arewa da a lokacin ba a ma riga an haifa ba, inda a ranar 15 ga watan Janairun, 1966 sojoji ‘yan ina da kisa a karkashin jagoracin Manjo Chukwuma Kaduna suka kashe su a kokarinsu na yi wa Janhuriya ta farko juyin mulki,” in ji shi.

Ya kara da cewa, a kokarin kungiyar na sake hada kan Arewacin Nijeriya, kungiyar ta ziyarci dukkan jihohin Arewa 19 inda ta gana da shugabannin al’umma da masu mulki da kuma matasa tare da neman hadin kansu wajen wayar da kan al’ummar Arewa da su falka su so juna su zauna lafiaya.