40 ga Ramalana
Al’adar Shehu Jaha a watan azumi ita ce, duk ranar da ya kai azumi sai ya jefa tsakuwa guda cikin wata buta da ya tanada, don gudun kada lissafi ya bace masa. Ran nan sai wata karamar ’yarsa ta ga ya jefa tsakuwar kamar yadda ya saba, da ya fita sai ta ciko hannunta da […]
Al’adar Shehu Jaha a watan azumi ita ce, duk ranar da ya kai azumi sai ya jefa tsakuwa guda cikin wata buta da ya tanada, don gudun kada lissafi ya bace masa. Ran nan sai wata karamar ’yarsa ta ga ya jefa tsakuwar kamar yadda ya saba, da ya fita sai ta ciko hannunta da tsakuwoyi ta watsa cikin butar. Ita a nufinta ta taimake shi ne wajen cika butar da tsakuwa. Ran nan suna hira da makwabtansa sai suka ce da shi: “Yau saura azuminmu nawa ne?” Sai ya ce: “Ban san abin da ya rage ba amma ina sane da kwankin da suka wuce na watan.” Daga nan sai ya tashi ya shiga gida. Da ya kirga tsakuwoyin da yake tarawa sai ya tarar da fiye da 120. A ransa ya ce: “Idan na fada musu wannan adadi dariya za su yi mini amma bari na rage zuwa Arba’in.” Sai ya fita ya ce musu: “Jama’a, yau azuminmu arba’in!” Makwabtan suka tuntsure da dariya, shi ma sai ya shiga taya su, ya kara da cewa: “Ai tsawo ne da wannan wata! To ashe da na fada muku ainihin kwanakin da suka shude a watan, da ban san irin dariyar da za ku yi ba.”
Daga Nasiru G. Ahmad