422. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce:

422. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya hana game da zarcen azumi, sai sahabbai suka ce, “Hakika kai kana aikatwa.” Ya ce: “Lallai ni, ba kamar ku nake ba, hakika ni […]

422. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce:
422. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce:

422. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya hana game da zarcen azumi, sai sahabbai suka ce, “Hakika kai kana aikatwa.” Ya ce: “Lallai ni, ba kamar ku nake ba, hakika ni ana ciyar da ni ana shayar da ni.”

423. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, dan Hadi ya ba mu labari daga Abdullahi dan Khabbab daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai shi ya ji Annabi (SAW) yana cewa: “Kada ku yi zarcen azumi, idan wani ya so ya yi zarce, to ya zarce zuwa lokacin sahur kadai.” Sai suka ce, “Amma hakika kai kana zarce ya Manzon Allah! Ya ce, “Lallai ni, ba kamarku nake ba, hakika ni, ina kwana da mai ciyarwa da ke ciyar da ni da kuma mai shayarwa da ke shayar da ni.”

424. An karbo daga Usman dan Abu Shaiba da Muhammad suka ce: “Abdatu ya ba mu labari daga Hisham dan Urwata daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya hana game da zarcen azumi don jin kai gare su (Musulmi). Sai suka ce, “Lallai kai kana zarcen.” Ya ce, “Hakika ni, ba kamar ku nake ba Ubangijina Yana ciyar da ni kuma Yana shayar da ni.” Abu Abdullahi (Bukhari) ya ce, “Usman bai ambaci cewa: “Domin jin kai gare su ba.”

Babi na Arba’in da Tara: Azabtar da wanda ke yawaita zarcen azumi. Anas ya ruwaito shi daga Annabi (SAW):

425. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Abu Salmata dan Abdurrahman ya ba mu labari cewa: “Lallai Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya hana game da zarcen azumi. Sai wani mutum daga cikin Musulmi ya ce, masa: “Lallai kai ma kana zarcen ya Manzon Allah!” Sai ya ce, “Wane ne kamata a cikinku? Hakika ni, ina kwana Ubangijina Yana ciyar da ni Yana shayar da ni.” Lokacin da suka ki hanuwa game da zarcen azumi. Sai (Annabi) ya yi zarce da su yini daya, sa’an nan ya kara yini, sa’an nan aka shiga watan (Shawwal).  Annabi ya ce musu a cikin bacin rai, “Da watan nan ya yi jinkiri da na kara muku wani yinin, don ya nuna musu bacin ransa lokacin da suka ki hanuwa.”

426. An karbo daga Yahya ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari daga Ma’amar daga Hammam cewa: :Lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, daga Annabi (SAW) ya ce, “Kashedinku da yin zarce, sau biyu, sai aka ce, “Lallai kai kana yin zarcen.” Sai ya ce, “Hakika ni, ina kwana Ubangijina Yana ciyar da ni Yana shayar da ni, ku rika sanya wa kawunanku aikin da kuke iyawa.”

Babi na Hamsin: Zarcen azumi zuwa lokacin sahur:

427. An karbo daga Ibrahim dan Hamza ya ce: “dan Abu Hazim ya ba mu labari daga Yazid daga Abdullahi dan Khabbab daga Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai shi ya ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Kada ku yi zarcen azumi, duk wanda yake son yin zarce a cikinku, to ya yi zarce zuwa lokacin sahur.” Sai suka ce, “Lallai kai kana yin zarce ya Manzon Allah! Ya ce, “Ni ba kamarku nake ba, hakika ina kwana da mai ciyarwa da ke ciyar da ni da kuma mai shayarwa da ke shayar da ni.”