6 ga watan Nuwamba za a rufe karbar sunayen gwarzon Afirka na Daily Trust

Ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2017 za a dakatar da rufe karbar sunayen wadanda aka zaba gwarazan Afirka na kamfanin jaridar Daily Trust. A sanarwar da babban jami’i a kamfanin Daily Trust, Aliu Akoshile ya sanyawa hannu ya ce kamfanin ya kara wa’adin ranar rufe karbar sunayen ne don a baiwa al’ummar Afirka damar […]

6 ga watan Nuwamba za a rufe karbar sunayen gwarzon Afirka na Daily Trust

Ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2017 za a dakatar da rufe karbar sunayen wadanda aka zaba gwarazan Afirka na kamfanin jaridar Daily Trust.
A sanarwar da babban jami’i a kamfanin Daily Trust, Aliu Akoshile ya sanyawa hannu ya ce kamfanin ya kara wa’adin ranar rufe karbar sunayen ne don a baiwa al’ummar Afirka damar zaben mutanen da suka cancanta.
Ya ce wajibi ne wanda aka zaba ya kasance ya yi wani aiki na taimakon al’umma cikin shekara guda daga 1 ga watan Oktoban shekarar 2016 zuwa ranar 30 ga watan Satumban shekarar 2017.