6 cikin kowane dalabai mata 10 an ci zarafinsu a jami’o’i 12 —Rahoto

Rahoton ya nuna a cikin duk dalibai mata 10, akalla mutum shida sun fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata a Jami’ar Bayero da wasu jami’o’i 11.

6 cikin kowane dalabai mata 10 an ci zarafinsu a jami’o’i 12 —Rahoto

Kashi 63 cikin 100 da dalibai mata a Jami’ar Bayero ta Kano da wasu jami’o’i a Nijeriya sun tabbatar da cewa sun fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata a makarantunsu.

Hakan na nufin a cikin kowadanne dalibai mata 10 akalla mutum shida sun fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata a jami’o’in da abin ya shafa.

Wani bincike binciken cin zarafi dalibai da kungiyoyin Alliance for Africa (AFA) da kuma Kwamitin Daraktocin Jinsi na Jami’o’in Nijeriya (CGDNU) suka gudanar ya bayyana cewa daliban da suka fuskaci cin zarafi ta hanyar lalata fito ne daga wasu jami’o’i 12 a yankunan Arewa da Kudancin Nijeriya.

“Wannan ya nuna yawaitar cin zarafin dalibai ya yawaita a manyan makarantun Nijeriya,” a cewar rahoton, wanda ya kara da cewa duk da haka, akwai wadanda aka ci zarafinsu da ba su bayyanawa saboda tsoron tsangwama da cin zalin wadanda suka keta musu haddi.

Daliban sun bayyana hakan ne a yayin amsa tambayoyin da masu binciken suka yi wa dalibai mata 3,528 a jami’o’in game kan cin zarafi ta hanyar lalata.

Jami’o’in su hada da Jami’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Jihar Kaduna da Jami’ar Abuja da Jami’ar Jihar Nasarawa da Jami’ar Jos  da Jami’ar Ibadan da Kuma Jami’ar Legas.

Sauran su ne Jami’ar Jami’ar Ibadan da Jami’ar Fatakwal da Jami’ar Jihar Delta da Jami’ar Fasaha ta Tarayya ta OWerri da Jami’ar Jihar Imo da Jami’ar Chukwueneka Odumegwu Ojukwu da ke Jihar  Anambra.

Babban Darakatar AFA, Iheoma Obibi, a yayin gabatar da sakamakon binciken ta ce, a yayin da ake tsammanin jami’o’in Nijeriya su zama cibiyoyin kare ilimi da samar da ƙwararrun, abubuwan da binciken ya gano ya nuna irin munanan abubuwan da dalibai mata ke fuskanta a yayin karatun jami’a, ba tare da an dauki wani kwakkwaran matakin yi wa tufkar hanci ba.

A ranar Litinin din nan ne aka sa ran fitar da cikakken rahoton wanda a ranar Lahadi, Daraktar Cibiyar Nazarin Jinsi da Al’amarun Mata ta Jam’ar Jos, Farfesa, Irene Agunloye da takwararta ta Jami’ar Bayero Dokta Safiya Ahmad Nuhu da sauransu suka fara bayarwa a ranar Lahadi.

Rashin aiki ya ƙaru zuwa kashi 4.3 a Najeriya — NBS

Mahara sun kashe mutane 30 a hare-haren Benuwe

An ɗaure matashi shekara 8 kan satar wayar taransufoma

An kama su kan fille kan ɗan acaɓa da sace baburinsa