Idan rai ya baci Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani labari ne mai taken; ‘Idan rai ya baci’ labarin na kunshe ne da yadda Manyan Gobe za su rika tunani kafin su bata ransu kan abin da bai taka kara ya […]
Idan rai ya baci
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani labari ne mai taken; ‘Idan rai ya baci’ labarin na kunshe ne da yadda Manyan Gobe za su rika tunani kafin su bata ransu kan abin da bai taka kara ya karya ba. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Akwai wani yaro mai yawan fushi. Daga an yi masa magana sai ya bata ransa. Wata rana sai mahaifinsa ya ba shi kusoshi da yawa. Ya ce da shi idan ransa ya baci, sai ya buga daya daga cikin kusoshin a bango har sai kusar ta nutse.
A ranar farko sai yaron ya buga kusoshi 37 a cikin bangon gini. Bayan mako 2, sai ya fara kokarin rage yin fushi saboda ba ya son kusoshin su taru su yi yawa. Har dai ya ga cewa ya kamata ya koyi hakuri.
Ana haka, sai wata rana yaron tun daga safiya har maraice bai buga ko kusa daya ba domin, ransa bai baci ba. Sai ya fada wa mahaifinsa cewa bai buga kusa a bango ba saboda yau ransa bai baci ba. Sai mahaifinsa ya ce masa a duk ranar da ransa bai baci ba, ya sa hannunsa a cikin bango ya cire kusa daya.
Hakan aka rika yi har ya ce da mahaifinsa kusoshin jikin bangon sun kare. Kuma a kan cewa ya koyi hakuri yanzu.
Sai mahaifinsa ya rike shi a hannu ya kai shi wajen bangon. Ya ce da shi “Ka yi kokari dana. Amma ka kalli ramummukan da ka haka a jikin bangon nan.” Bangon ba zai taba canjawa ba. Haka kuma idan ka fadi magana, maganar na nan kamar tabo wanda ba za ta taba canjawa ba.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labari. Domin idan rai ya baci bai kamata hankali ya gushe ba. Ya kamata a zama masu hakuri da kuma sanin irin furucin da ya kamata a rika furtawa ko da rai ya baci.