Burina in rika tallafa wa marasa galihu – Hajiya Nafisa Abubakar Zaki Hajiya Nafisa Abubakar Zaki ita ce Daraktar Gidauniyar Al-Mizan Foundation da ke Sakkwato. Ta kafa gidauniyar ce don tallafa wa al’umma musamman masu rauni.  Ta taba zama Darakta a Cibiyar Koyar da Sana’o’in Hannu ta matar Gwamnan Jihar Sakkwato, Hajiya Mariya Tambuwal Debelopment […]

Hajiya Nafisa Abubakar Zaki

Burina in rika tallafa wa marasa galihu

– Hajiya Nafisa Abubakar Zaki

Hajiya Nafisa Abubakar Zaki ita ce Daraktar Gidauniyar Al-Mizan Foundation da ke Sakkwato. Ta kafa gidauniyar ce don tallafa wa al’umma musamman masu rauni.  Ta taba zama Darakta a Cibiyar Koyar da Sana’o’in Hannu ta matar Gwamnan Jihar Sakkwato, Hajiya Mariya Tambuwal Debelopment Initiatibe kafin ta bude tata cibiyar.  A zantawarta da Aminiya ta tabo tarihinta da nasarori da kuma irin kalubalen da ta fuskanta a rayuwa.

 

Tarihina:

Sunana Nafisa Abubakar Zaki. Ni haifaffiyar Jihar Sakkwato ce, daga Karamar Hukumar Tambuwal.   An haife ni a ranar 8 ga watan Disamban 1981.  An sanya ni a firamaren Jami’ar Usman Dan Fodiyo.  Bayan na kammala sai na wuce Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnati da ke Sakkwato (GGC). Na samu digiri na farko a Jami’ar Usman Danf Fodiyo a fannin ilimi da kimiyyar halittu sai na biyu  kan jinsi da bunkasa ci gaba.

Abin da na fi mayar da hankali a kansa:

Ni mace ce mai son ganin ci gaban al’umma, ni malama ce mai kokarin zaburar da al’umma ga neman hakkinsu da ci gabansu musamman a bangaren kare hakkin mata da ilimantar da su da wayar da kan jama’a, kan cuta mai karya garkuwar jiki (kanjamau)  da taimakon marayu da gajiyayyu da kwato hakkin talaka da sauran abubuwan jinkai na rayuwa.

 

Nasarorin da na samu:

Na yi aiki a wurare da dama, irin Sakandaren Tunawa da Sardauna Ahmadu Bello da Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da Jami’ar Usman Danf Fodiyo da Bankin Duniya da MARCH da KiCEI da dRPC da NEI da USAID. Kuma ni ce tsohuwar Daraktar Zartawa a Gidauniyar Uwargidan Gwamnan Jihar Sakkwato, Mariya Tambuwal Debelopment Initiatibe, kuma Shugabar Gidauniyar  Taimakon Jama’a ta Al-Mizan. Na yi aiki a wasu wurare sun fi 10 da ban ambata ba.

Ilimi da fahimtar da na samu a wadancan wurare, sun karfafa ni har na kai inda ban zaci zan kai ba.   Na yi aiki da mutane a kasar nan da wajenta, kofofin alheri suna ta budewa kan duk abin da zan yi zan tsaya kai da fata in yi shi tsakani da Allah hakan ya taimake ni na kai matsayin da ban taba zata a rayuwata ba.

Na samu nasarori sosai a rayuwata musamman a bangaren karramawa da karo karatu da ayyukan yi da kyautar kudi da taimakon mutane ga matsalolinsu. A gaskiya mutane sun amfana da gudunmawata.

Sannan na samu damar koyar da dubban  mata da matasa maza da marayu da yara marasa galihu ta fannoni da dama da suka hada da sana’o’in hannu da daukar nauyin karatun  dimbin matasa inda a yanzu haka da yawa daga ciki sun kammala karatu a jami’a da Kwalejin Ilimi da Kwalejin Kimiyya da Kere-kere da sauransu duk a Jihar Sakkwato. Da yawa daga cikin irin wadannan yara yanzu haka sun samu aiki a ma’aikatu da hukumomin jiha da wasu kungiyoyi masu zaman kansu.

 

Kalubalen da na fuskanta:

A rayuwa, dole a fuskanci kalubale a matakai daban-daban. Na yi sa’a na kammala karatuna kafin in yi aure, ban da wata hujja da zan damu da lokacin aikina. Bayan na yi aure, abin da ya ba ni wahala shi ne yadda zan raba lokacin aiki da na iyalina, ya dauke ni tsawon lokaci ina fama kafin in daidaita su. Dole sai da na sadaukar abin da na fi so a rayuwata wato taimakon al’umma na dauki kula da tarbiyyar iyalina. Hakurin da na yi  da jajircewata da fahimtar da nake da ita su ne suka taimake ni na aiwatar da wasu abubuwa da nake kudiri a cikin al’ummata a bangarori daban-daban na rayuwa.

Daya daga cikin abin da ya taimake ni na samu nasarar kalubalen da na fuskanta a rayuwa shi ne goyon bayan da iyalina suka ba ni musamman mijina Dokta Aminu Halliru Bunza, Sardaunan Bunza na farko.  A gaskiya ina yi masa godiya don ba ya ba ni hadin kai da goyon baya da hakan ya sa na samu nasara a rayuwa. Mun samu ’ya’ya biyu tare da shi. Allah ne kadai Zai biya shi abubuwan da ya yi mana.   Fatana ya samu Aljannar Firdausi.

 

Abubuwan da nake son a rika tunawa da ni:

Ina son a tuna da ni bayan ba ni, da kyakkyawan aikin da na aiwatar a rayuwata. A kowane lokaci ba ni da burin da ya wuce na faranta wa al’umma rai. Ba ni da burin da ya wuce in ga mutum yana cikin farin ciki, ya yi rayuwarsa ya samu abin da ya ci, ya samu ilimi da lafiya, duk abin da nake yi ba don kaina nake yi ba.

Hajiya Nafisa tare da maigidanta da ‘ya’yansu biyu

Matar da nake koyi da ita:

Macen da nake koyi da ita. ita ce Hajiya Hauwa’u Abubakar, mahaifiyata. Gare ta na koyi dimbin abubuwan rayuwa kamar dabi’ar hakuri, mutunta jama’a, saukin kai, gaskiya, kaifin tunani, samun gamsuwa a cikin rayuwa ga duk abin da ka samu da sadaukarwa da soyayya da kulawa da sanya fahimta ga lamarin rayuwa da shiga cikin harkokin kasuwanci da sauransu. Uwa ce da kowane da ke son ya samu irinta.

 

Shawarwarina ga mata:

Shawararwarin da zan bai wa mata ba za su fi wadannan ba:

  1. Mata ya kamata su zama masu iya dogaro da kansu su rage kwanciya komai sai an yi musu, su fito da hanyoyin rage talauci a cikin al’ummarsu. Na tabbata in tattalin arzikin mata ya karu tsananin talaucin da ake fama da shi zai ragu, cima-zaune da tayar da hayaniya a cikin al’umma za su ragu sosai.
  2. Mata su sani su ma mutane ne, su yi amfani da baiwar da Allah Ya ba su, su shiga a dama da su wajen ciyar da kasar nan gaba. Duk da dai maza sun mamaye komai a wurin rabon mukamai ba shi zai sa mata ba za su hada kansu ba, su tallafi junansu.
  3. Mata su samu fahimtar juna a tsakaninsu, a jefar da duk wani bambanci da ake gani akwai tsakaninmu, tarihi ya bayyana akwai mata magabata da suka taka rawa a ci gaban al’umma, ba dalilin da zai sa mu koma baya.
  4. Dole ne mata su karbi canjin da aka samu, su yi ilimi, su san kansu, su taimaki mazansu, su mayar da hankali ga abin da ke faruwa da su a kullum, su koyar da ’ya’yansu sosai, su zama garkuwa ga duk wani abu da zai cutar da su.
  5. Mata ya kamata ku sani ku ne masu hajoji amma kun zama matalauta don kun ki yarda da baiwar da Allah Ya ba ku, dole ku fito da kasuwancin da zai taimake ku. A Arewacin Najeriya musamman a jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara duk wani karamin kasuwanci da ake yi mata ke tafiyar da shi, sauran mata ya kamata ku tashi tsaye don kara habaka tattalin arzikin kasar nan.
  6. Mata su dauki halayyar zuwa a asibiti ana duba lafiyarsu don a tabbatar kina da lafiya. Ya kamata mata su rika zuwa asibiti lokaci zuwa lokaci ana duba lafiyarsu kamar ciwon daji, cuta mai karya garkuwar dan Adam, ciwon hawan jini, ciwon suga da sauransu. Hakan zai sanya mace ta kara zama cikin kwanciyar hankali. In aka duba ki kina da wata cuta a dauki mataki da sauri zai taimake ki sabanin ciwo ya yi nisa.