Kungiyar kwadago ta bukaci a fara biyan albashin Naira dubu 30
Ma’aikatan Najeriya sun bukaci gwamnati ta gaggauta fara biyan sabon tsarin mafi karancin albsashin ma’aikata na Naira dubu 30 kamar yadda shugaba Buhari ya rattaba hannu akai. Shugabannin kungiyoyin kwado na Najeriya NLC Ayuba Wabba da shugaban kungiyar TUC Bobboi Bala Kaigama suka sanar a yau Laraba yayin gudanar da taron ranar ma’aikata a dandalin […]
Ma’aikatan Najeriya sun bukaci gwamnati ta gaggauta fara biyan sabon tsarin mafi karancin albsashin ma’aikata na Naira dubu 30 kamar yadda shugaba Buhari ya rattaba hannu akai.
Shugabannin kungiyoyin kwado na Najeriya NLC Ayuba Wabba da shugaban kungiyar TUC Bobboi Bala Kaigama suka sanar a yau Laraba yayin gudanar da taron ranar ma’aikata a dandalin Eagle Square da ke Abuja.
Kungiyoyin sun yabawa majalisar dokokin Najeriya da shugaban Najeriya na amincewa akan sabon tsarin biyan mafi karancin albashin Naira dubu 30 da za a fara.