Mangal zai gina kamfanin casar shinkafa na Dala miliyan 50 a Katsina Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina A karshen makon jiya ne Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi bikin aza harhashin ginin katafaren kamfanin casa da surfe shinkafa mai suna ‘Darma Rice Mill Limited’ da zai ci kimanin Dalar Amurka miliyan […]
Mangal zai gina kamfanin casar shinkafa na Dala
miliyan 50 a Katsina
Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina
A |
karshen makon jiya ne Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi bikin aza harhashin ginin katafaren kamfanin casa da surfe shinkafa mai suna ‘Darma Rice Mill Limited’ da zai ci kimanin Dalar Amurka miliyan 50 (kimanin Naira biliyan 15.2) wanda hamshakin dan kasuwar nan Alhaji Dahiru Bara’u Mangal zai gina a kan hanyar zuwa Dutsinma da ke Katsina.
Idan aka kammala ginin kamfanin, zai zamo na farko irinsa da manoman shinkafa a jihar za su amfana da shi fiye da saura.
Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Aminu Bello Masari ya tabbatar wa masu son zuba jari a jihar cewa gwamnatinsa za ta ba su cikakken hadin kai da goyon baya, domin ganin sun cimma nasarar shirye-shiryen da gwamnati ta fito da su don aiwatarwa.
Gwamna Aminu Masari ya ce, irin wannan hobbasa ake bukata daga masu dukiya domin ciyar da jihar da kasa baki daya gaba. Gwamnan ya kara da cewa duk mai kishin jihar da al’ummarta dole ya yi farin ciki da wannan aiki mai cike da dimbin alherai ciki kuwa har da samar da aikin yi ga jama’a sannan kuma ga tarihi an bari.
Da ya juya ga wanda ya assasa wannan kamfani, Gwamna Aminu Bello Masari ya yi jinjina tare da yabo ga Alhaji Dahiru Mangal, domin kishi da sadaukarwar da ya nuna wajen amsa kiran da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake ta yi a fito a rungumi harkar noma domin ita ce kadai mafita ga kasar nan.
Babban Daraktan Kamfanin, Injiniya Faisal Dahiru Mangal ya ce aikin kamfanin zai ci kimanin Dalar Amurka miliyan 50, kuma zai samar da ayyukan yi akalla dubu 10 a tsakanin al’umma.
Ya kara da cewa za su gina wani kamfanin yin takin zamani mai suna Gobarau Agro Allied Limited wanda shi kuma zai ci kimanin Dala miliyan biyar bayan tarin ayyukan da zai samar ga al’umma.
Injiniya Faisal Mangal ya kara da cewa, akwai kwararru daga kasar Indiya a karkashin jagorancin Mista Mehul Ramwani da za su yi aikin domin ganin an tabbatar da samun nasarar da ake bukata.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin wadansu daga cikin mahalarta taron inda suka nuna cewa, samar da wadannan kamfanoni zai kara zaburar da manoma ta fuskoki da dama. Hakan zai sake fitar da sunan Jihar Katsina a sauran duniya musamman ta fuskar noma.