Allah Ya jikan Umar Sa’idu Tudun Wada (UST) 1960 zuwa 2019 I nna lillahi wa’inna ilaihi raji’un! Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un!! Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un!!! Malaman addinin Musulunci kan fassara mana wannan aya ta sama da cewa “Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.” Allah (SWT) Ya yi gaskiya, wannan aya […]

Allah Ya jikan Umar Sa’idu Tudun Wada (UST) 1960 zuwa 2019

I

nna lillahi wa’inna ilaihi raji’un! Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un!! Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un!!! Malaman addinin Musulunci kan fassara mana wannan aya ta sama da cewa “Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.” Allah (SWT) Ya yi gaskiya, wannan aya ta tabbata a kan amini kuma abokin aiki Malam Umar Sa`idu Tudun, wanda muke kira a takaice da UST.  Allah (SWT) Ya karbi ransa a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da shi da matarsa Malama A’ishatu Sule mai rikon mukamin Manajar Daraktan Gidan Rediyon Jihar Kano da ’yarsa Malama Maryam da direbansa Malam Ado Gauta a daf da garin Kura da ke Jihar Kano a kan hanyar Kano zuwa Zariya a ranar Lahadin da ta gabata.

Shi kadai Allah Ya karbi ran nasa, bayan wancan hadari, kasancewar matar da ’yar da shi kansa direban, duk tsamin jiki suka samu a hadarin, don haka dukkansu ba wanda ya kwana a asibiti a ranar.

An haifi UST, a garin Tudun Wadan Dankadai a Jihar Kano a 1960, inda nan ya yi karatun firamare, sannan ya zarce zuwa shaharriyar makarantar sakandaren gwamnati da a yau ake kira Kwalejin Rumfa, Kano, kwalejin da ya kammala a 1979.

Kammala Kwalejin Rumfa ke da wuya, sai Malam UST, ya samu aikin koyarwa a makarantar firamare ta garin Wudil, aikin koyarwar da bai dade a ciki ba, sai ya samu aikin jarida da tashar talabijin ta kasa, wato NTA, Kano a 1980. Daga bisani kuma sai  gwamnatin farar hula ta Jihar Kano ta marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, ta kafa gidan talabijin da a yau ake kira tashar Talbijin ta Muhammadu Abubakar Rimi, inda UST, ya dawo da aiki a 1983.  A tashar ce UST, ya yi aikin jarida na kusan shekara 20. A nan tauraruwarsa ta fara haskawa a kan aikin jaridar na alheri da a yau ake ambatonsa da aikatawa a cikin shekara 39 da ya yi a cikin aikin.

Malam UST, zakakurin dan jarida ne da Allah Ya ba shi daukakka da matukar nasara a cikin aikin, a ciki da wajen kasar nan, har ya yi sunan da ko da digirin-digirgir mutum ya karanta a fannin sai haka. Alhali shi a cikin aikin ma ya samu karamar Difloma a fannin jarid, sai kuma kananan tarurruka da kwasa-kwasai da ya yi ta halarta, wani lokaci ma da kudinsa. Har  gidan Rediyon Muryar Amurka da ke birnin Washington DC ya yi aiki na kusan shekara uku, (2006 zuwa 2009), aikin da bisa kashin kansa ya rubuta takardar  ajiyewa ya dawo gida, al’amarin da ke da matukar wuya ko a shekarun baya, balle a yau. Ya taba zama wakilin  Rediyon Jamus a Kano.

UST, ya ajiye aiki da gidan Rediyon Amurka, bisa ga damuwar da yake da ita a kan baya tare da mahaifiyarsa, wadda ta manyanta, don haka ya gwammace ya dawo kusa da ita, don ba ta cikakkiyar kulawa.

Da yake yana da rabon hakan, ya dawo din ya kuma dauko ta daga Tudun Wada ya dawo da ita gidansa a Kano, inda a nan Allah Ya karbi ranta, bayan kusan shekara bakwai da dawowarsa.

Kamar yadda Alhaji Ahmed Aminu, tsohon Babban Sakatare a gwamnatin Kano kuma tsohon Janar Manaja a tashar talabijin ta Jihar Kano, wato CTB67, tun a 1984, da ya zo tashar ya gane hazaka da sadaukarwa da hakuri da rayuwa da neman sanin aiki ba kosawa irin na marigayi UST da kuma marigayi Malam Umar Dutse Mahammed Janar Manaja na farko na gidan Rediyon Freedom, Kano, a lokacin da suke tashar talabijin ta CTB67.  Ya ce kuma tun a lokacin suke mutunci da tuntubar juna da ma yin aiki tare da marigayi UST, bisa ga irin kwazo da biyayya da gudun abin duniya irin na UST.

Ya kuma bayyana marigayin da cewa mutum ne mai akidar kansa da kan dauki mataki a kan dukkan abin da ya ga ba daidai ba ne don neman gyara, ba tare da shayi ko jin tsoron wa abin zai shafa ba, amma cikin kamanta gaskiya da adalci.

A cikin watan Disamban 2017, Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya nada marigayi UST a matsayin Manajin Daraktan Gidan Rediyon Kano, bayan abubuwa sun tabarbare a gidan.

A dan zaman da ya yi na kusan shekara daya da rabi, marigayi UST, bayan farfado da tashoshin rediyon biyu, AM/FM, ya kuma bullo da sababbin shirye-shirye masu ilimantarwa da nishadantarwa da kayatarwa, baya ga dukufa da ya yi wajen biyan ma’aikatan wucin-gadi dimbi alawus-alawus da suka dade suna bi. Ya kuma gina sabon dakin watsa shirye-shirye da mayar da wadansu ma’aikata da suka shafe shekaru  a zaman wucin-gadi zuwa na dindindin. Wadansu ma’aikata da suka yi ritaya a take ya sa aka ba su kwantaragin ci gaba da aiki na shekara biyu, abin da da ba a taba yi ba. Kusan dukkan kayayyakin aiki sun samu tagomashi, haka ma’aikata sun dawo cikin hayyacinsu na yin aikin jarida yadda ya kamata.

Don a rika samun hadin kan aiki tare tsakankani kafofin watsa labarai da ke Kano  ya sanya marigayi UST ya shige gaba aka kafa wata kungiya ta shugabannin gidajen rediyon, wanda shi ke shugabanta, inda sukan tattauna a kan matsalolin da ke bijiro musu da yadda za su rika shawo kansu.

A bara yana daga cikin wadanda suka shige gaba wajen ganin gwamnatin Jihar Kano ta gabatar da taron wayar da kan ’yan siyasa (sojojin baka), masu magana kowace iri a kafofin watsa labarai da nufin ganin an wayar da kan mutanen kan yadda ya kamata su rika ba da gudunmawa a siyasa.

Ba wai a kan aikin jarida alheri da kamantawar marigayi suka tsaya ba, hatta ya yi fice a kan yadda yake girmama manya da kanana da kokarin yin zumunci ta hanyar shiga harkokin jama’a da ba da taimako ga mabukata, ba tare da la’akari da ya sanka ko bai sanka ba.

Abokansa na kuruciya wadanda suka yi karatun firamare ko sakandare ko na farkon kama aiki, kai ko wadanda aka hadu ta wata hanyar, duk sun bayar da kyakykwar shaida a kan marigayi UST. Sai dai mu yi masa fatan Allah Ya sada shi da rahamarSa, Ya sa Aljanna Firdausi ce makomarsa, Ya kuma duba bayansa.

Saura da me? Wannan fili yana kira ga ’yan uwa ’yan jarida da abokai da aminan marigayi UST da ma sauran dukkan al’umma masu kwadayin samun lada, a kan mu hadu mu yi wani yunkuri ta yadda za a kafa wata GIDAUNIYA da za ta rika daukar dawainiyar zuriyar da marigayi UST ya bari, ko da a kan magungunansu da karatunsu. Abin da ya sa na yi wannan kira bai wuce irin yawan iyalin da ya bari ba, wadda ta kunshi matan aure uku da ’ya’ya 22 daga cikinsu har da jariri Al-Amin da marigayi ya san an haife shi har ya yada wa duniya, amma bai ga sunansa ba. Allah Ya ba da iko mu taimaka. Daga karshe ina kara addu’ar Allah (SWT) Ya gafarta wa UST tare da duba bayansa, amin summa amin.