Takaddamar soyayya: Tsakanin maza da mata, wa ya fi rikon alkawarin soyayya (4)
Har yanzu dai muna cikin maudu’in da ake ragargaza takaddama tsakanin maza da mata, domin gano wadanda suka fi rikon amanar soyayya. A wannan makon ma ga sakonnin da muka samu, sai mu cala: Ibrahim Hamisu Kano (08188966748), ga nasa bayanin: “Gaskiya ni ina ganin maza sun fi rike amanar soyayya, dalilina shi ne: Yadda […]
Har yanzu dai muna cikin maudu’in da ake ragargaza takaddama tsakanin maza da mata, domin gano wadanda suka fi rikon amanar soyayya. A wannan makon ma ga sakonnin da muka samu, sai mu cala:
Ibrahim Hamisu Kano (08188966748), ga nasa bayanin: “Gaskiya ni ina ganin maza sun fi rike amanar soyayya, dalilina shi ne: Yadda za ka ga ’yan mata kudi suna saurin juya tunaninsu. Za ka ga yarinya kuna tsaka da soyayarku rimi-rimi, da wani mai kudi ya zo ya jika ta da Naira, to fa shi ke nan sai ta daina son ka. Wani lokacin iyayen ake wa ruwan Naira, su kuma sai su juya tunanin yarinyar ta karkata ga mai kudin. Shi kuma namiji za ka ga komin wuya ko dadi, makukar yana son mace; to fa yana nan a kan bakansa, da wahala ka ga ya canja. Don haka nake ganin mamiji ya fi mace rike amanar soyayya.”
Shi ma Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu, Gusau (08069807496), ya goyi bayan maza ne, inda yake cewa: “FDK, ai ko kusa ba a taba hada tsakanin maza da mata a kan rike alkawarin soyayya. Domin da yawa daga cikin maza suna iya rike mace daya suna soyayya da ita na tsawon lokaci, tun ba ta da wayo har ta kai wani matsayi a rayuwa, amma dare daya za ta iya juya maka baya. Hakan ya sha faruwa bila’adadin a garuruwanmu, in har kai ba a yi maka ba to an yi wa na kusa da kai ko dan uwanka.”
Kamar hadin baki, shi ma Abubakar Suleiman Charanchi (08034626452), mazan ya goya wa baya da cewa: FDK, da fatan kana lafiya. A gaskiya ’yan mata suka fi yaudarar samari saboda za ka samu yarinya kana sonta tsakani da Allah, ka rike amana amma sai ka ji ta canja sheka da wani wanda ya fi ka kudi. Sai ka ji an ce shi za a ba, ka ga ai ba a yi ma adalci ba.”
Khairat Baba Ahmad (09065190426) ta ce: “Aminci, tsira, daraja, rahama, imani, su tabbata ga duk wanda ya tsinci kansa a cikin Musulunci. Bayan gaisuwa da fatan alheri ga jaridar Aminiya da kuma wannan shafi na FDK mai albarka. Ina son tofa albarkacin bakina game da wannan muhawara da ake yi. A nawa ganin ko in ce a nawa ra’ayin, gaskiya maza sun fi rikon amana da kuma sanin darajar soyaya saboda gaskiya mace koda an sa ranar aurenta da namiji; hakan ba zai hana ta hulda da maza ba, amma namiji yana iya hakura ba zai nemi wata ba, domin ya san darajar so amma ita mace sai a hankali gaskiya.”
Is’hak Sani Junaidu Apapa-Legas (08143983072): “Ina kira ga iyayen ’yan mata su hana ’ya’yansu yin soyayya da samari. Sai saurayi ya ce zai auri ’yarku, sai ku aminta har a rika ba su daki su rika hira ba tare da yaro mai wayo a kusa ba. Wani saurayi ya ce yana son kanwata, mamana ta amince ya rika zuwa hira wurinta, ya yi mata karyar zai aure ta. Ashe ba haka ba ne, ya ci amanarta. Bayan ya tafi sai ta kamu da rashin lafiya. Ashe tsafi ya yi da ita, tsutsa ta rika fita ta farjinta har ta mutu. Shi kuma an neme shi an rasa, ba a gan shi ba, ya gudu. Iyaye, a kula don Allah!”
Amiru Isah Bakori, Tashar Guga (08084213547): “FDK, mata sun fi maza rikon soyayya. Mace na iya jiran mutum ya gama karatu ko ta jira ya samu sauki in bai lafiya. In mace ta koma gidansu kan rashin lafiya, Allah-Allah take sauki ya samu ta dawo. Mace na iya sayar da gonar gado ko kayan dakinta ta ba miji jari amma shi bai iya sayar da gona don ita. Duk aikin assha da miji ya yi, in an fada wa matarsa sai ta karyata. Wadansu mazan su gudu zuwa bariki, wadansu a kai su gidan yari, wadansu bashi ya kore su amma matan na nan zaune har sai sun dawo. Mata sun fi maza alkawari, ni shaida ne. Na nemi aure ba a ba ni ba sai aka ba wani amma da yake ’yar wahala ce, wallahi cikin ’ya’yan da ta haifa akwai mai sunana. Ni tuntuni na manta da ita amma ita har yau ina zuciyarta. Wadansu mazan duka, zagi, cin mutunci, wulakanci iri-iri, karancin abinci, ba cefanen kirki, ga karancin sutura, ba dakin kirki, ba ban-daki, kullum yawon haya, kullum cikin babu amma matan suna nan like da su har ma su yi fushi, in an fadi laifin mazansu. FDK kada ka raba daya biyu, mata sun fi rikon alkawarin soyayya.
Rahmat Ukkshatu Muhammad Manaja Kontagora (09071955061): “Gaskiya abin da zan ce shi ne, mafi yawan ’yan mata suna shigar banza. Akwai wadanda za su fita da hijab a gida amma da zarar sun fita sai ka ga sun cire shi, da ma kayan banza suka saka wadansu kuma kawaye ke bata su, wadansu kuma sakacin iyaye ne; wadansu kuma yawan kallace-kallace ke sa su ce sai sun yi koyi da abin da suka gani a fim. Allah Ya sa mu dace kuma Ya shirye mu, amin.”
Shi kuwa Abubakar Adamu Azara (08024083571), martani ya mayar game da kalaman Anisa Abdullahi Adamu, ya ce: “Karya alƙawari sai mata, rusa soyayya sai mata. Su ne ke son mutum tsakani da Allah amma sai in da kudi alƙawarin soyayya za su iya ɗorewa, Malama Anisa ’yar mutanen Daura. Hatara dai!”
Saddik J.M.T Suleja (07012115752): “FDK, ni bako ne wurin tofa albarkacin bakina amma ni ba bako ne cikin fadarka ba. A gaskiya ɓangaren alƙawarin soyayya a ba maza wuri. Mata nawa ake kai lefe a watsar, mata nawa masu hali suke raba su da masoyansu na gaskiya? Ai in ana batun alƙawarin soyayya, kada ma mata su motsa saboda ƙalilan ne masu kwatantawa.”
Daga Muhammad Regede: “Fatan alheri gare ka FDK, duk mako sai na duba filimmu a jarida. Ni a guna maza sun fi mata rikon alkawari saboda mace sai ta tara maza goma ta yi ta yawo da hankalinsu.”