Ya kashe saurayin ’yarsa ya aure ta

Wani mutum a West Birginia a kasar Amurka ya shaida wa hukumomi cewa ya auri  daya daga cikin ’ya’yansa biyu bayan ya taimaka wajen kashe saurayin daya daga cikinsu tare da binne gawarsa a wani kabari da suka gina. Larry Paul McClure, mai shekara 55 ya fadi a cikin wata wasika da ya aike wa […]

Ya kashe saurayin ’yarsa ya aure ta

Larry Paul McClure da ‘yarsa Amanda da ya aura

Wani mutum a West Birginia a kasar Amurka ya shaida wa hukumomi cewa ya auri  daya daga cikin ’ya’yansa biyu bayan ya taimaka wajen kashe saurayin daya daga cikinsu tare da binne gawarsa a wani kabari da suka gina.

Larry Paul McClure, mai shekara 55 ya fadi a cikin wata wasika da ya aike wa hukumar bincike a jihar cewa shi da ’ya’yansa, Amanda Michelle McClure mai shekara 31 da Anna Mari Choudhry mai shekara 32 sun hada baki inda suka kashe John McGuire, wanda saurayin Amanda ne.

Wani jami’in ’yan sanda a Jihar West Birginia ya bada shaida a zaman kotun da aka gudanarwa cewa mutum uku da ake zargi sun doka wa McGuire kwalbar giya ce a kai daga bisani suka daure shi tare da yi masa allurar guba kamar yadda bincike ya gano.

Daga nan sai suka shake shi har sai da ya mutu daga bisani kuma suka haka kabari suka binne shi a cikin gidan da suke zaune a garin Skygusty da ke cikin jihar.

A cikin wasikarsa, McClure ya bayyana cewa sun yi kisan ne bayan ’yarsa Amanda ta kawo shawarar haka.

“Ba zan iya fadar dalilin da ya sanya Amanda take son John McGuire ya mutu ba,” Larry McClure ya rubuta a cikin wasikar. Ya kara da cewa “Wannan ba zai wahalar ba ga duk iyalaina da iyalan John McGuires.”

’Yan sanda sun yi zargin cewa Amanda da mahaifinta sun tafi Birginia inda suka yi aure a cocin United Methodist Church.

Larry McClure, wanda sunansa ya yi kauri wajen cin zarafi, ya ci gaba da zaman aure da ’yarsa a gidan da suka kashe McGuire, kamar yadda rahoton ya ce.

A  yanzu ana tuhumar McClure da ’ya’yansa da laifin kisan kai.