83% na alhazan bana da suka rasu satar hanya suka yi —Saudiyya
A cikin duk alhzai 10 da suka rasu a yayin aikin Hajji bana, akalla mutum takwas sun je ne ta barauniyar hanya
Ma’aikatar Lafiya ta kasar Saudiyya ta bayyana cewa a cikin duk alhzai 10 da suka rasu a yayin aikin Hajji bana, sama a mutum tsakuwa sun gudanar da Hajji ne ta barauniyar hanya.
Ministan Lafiya na Saudiyya, Fahad bin Abdurrahman Al-Jalajel, ya bayyana cewa rashin cikakkun takardun aikin Hajji ya tilasta wa alhazan da abin ya shafa zuwa Saudiyyan a kafa cikin tsananin zafin rana ba tare da hutawa ko samun wurin fakewa ba.
Ya bayyana cewa irin wadannan alhazai sun yi wannan doguwar tafiya mai hatsari ne duk da cewa yawancinsu tsofaffi ne da masu fama da rashin mai tsanani.
Ministan ya bayyana cewa a halin yanzu mutum 95 daga cikin irin wadannan alhazai matsa takardu da ke kwance a asibiti an wuce da su Riyadh, babban birnin kasar domin ci gaba da jinyar su.
- Kano: ’Yan sanda sun kori ’yan tauri daga Fadar Sarki
- Adadin Alhazan da suka mutu ya haura 1,000 a Saudiyya
Ma’aikatar ta sanar nuna daga cikin mahajjata 465,000 da suka samu kulawa a asibiti a kasar a bana, 1,301 sun rasu.
Sama da 550 daga cikin alhazan sun rasu ne sakam tsananin zafin da ya kai maki 51.8 a ma’aunin Celcius.
Sama da 600 daga cikin jimillar mamatan ’yan kasar Masar ne, 60 daga Jordan yayin da Iran ke da 5 daga cikin wadanda suka rasu a sakamakon cututtuka masu alaka da zafi.
Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce, mutum uku ne suka mutu a lokacin aikin Hajji, wanda hakan ya sa adadin mahajjatan Najeriya da suka mutu a Saudiyya ya kai 15.
Alhazai kimanin miliyan daya da dubu dari takwas ne suka sauke farali a bana.