Sojoji sun saki wakilin Daily Trust da suka kama a Maiduguri

Rundunar sojojin Najeriya ta saki wakilin jaridar Daily Trust mai suna Olatunji Omirin da ta kama a yammacin yau Alhamis a birnin Maiduguri.  Sojojin su uku, biyu cikin kayan gida daya cikin kaki, sun kama Olatunji ne da misalin karfe 4:40 na yamma. Sun fara zuwa ofishin shiyya na Daily Trust da ke hanyar Baga […]

Sojoji sun saki wakilin Daily Trust da suka kama a Maiduguri

Rundunar sojojin Najeriya ta saki wakilin jaridar Daily Trust mai suna Olatunji Omirin da ta kama a yammacin yau Alhamis a birnin Maiduguri. 

Sojojin su uku, biyu cikin kayan gida daya cikin kaki, sun kama Olatunji ne da misalin karfe 4:40 na yamma.

Sun fara zuwa ofishin shiyya na Daily Trust da ke hanyar Baga ne sau biyu, kafin daga baya suka je cibiyar, inda suka kama shi suka tafi da shi.

Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Borno ta nuna bacin ranta tare da yin Allah-wadai da kama dan jaridar, inda ta ce wannan “cin mutuncin dimokuradiyya ne da kuma aikin jarida, wanda ke maimaita kansa bayan faruwar irin hakan shekara guda da ta wuce”.

Ita ma kungiya mai kare hakkin ‘yan jarida a duniya CPJ ta nuna kaduwarta kan kama Olatunji, inda ta tuna makamancin wannnan lamari na ranar 6 ga watan Janairun 2019 yayin da sojojin suka dirar wa ofishin Daily Trust na Maiduguri da na Abuja kuma suka kama wasu editoci.

Idan ba a manta ba, yau shekara daya da kwana 23 ke nan daidai da sojoji suka je ofishin kamfanin na Maiduguri, inda suka kama Editan shiyya na ofishin da wani wakilin Daily Trust din, Ibrahim Sawab.