Wacce asara ‘yan sanda suka yi a farmakin da suka kai Kaduna?
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce an kashe mata jami’i guda daya mai mukamin sufeto sannan aka raunata wasu 13 a samamen da ta kai kan sansanin kungiyar Ansaru. A ranar Laraba ne rundunar ta ce ta kai harin a dajin Kuduru da ke Birnin Gwari na jihar Kaduna, inda ta “kashe ‘yan bindiga 250”. […]
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce an kashe mata jami’i guda daya mai mukamin sufeto sannan aka raunata wasu 13 a samamen da ta kai kan sansanin kungiyar Ansaru.
A ranar Laraba ne rundunar ta ce ta kai harin a dajin Kuduru da ke Birnin Gwari na jihar Kaduna, inda ta “kashe ‘yan bindiga 250”. Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.
Rundunar ta kume ce jirginta mai saukar angulu ne kadai aka kai wa hari kuma matukansa ba su ji manyan raunuka ba.
Amma wata sanarwa da rundunar ta fita a ranar Alhamis ta ce Sufeto Muhammed Abubakar ya mutu a
asibiti bisa raunin da ya ji yayin artabun na ranar Laraba.
Sannan ta bayyana sunan wasu “kasurguman kwamandojin ‘yan bindigar” da ta ce ta yi nasarar kashewa.
“An kashe Haruna Basullube, wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, da kuma wani babban mai satar shanu Bashir Leta, yayin da kuma aka raunata wani kwamandan Boko Haram Mallam Abba da kasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Mofa”.
Sanarwar ta bayyana Sufeto Muhammed Abubakar da cewa kwararren dan sanda ne na rundunar musamman ta Police Special Forces, wanda ya samu horo a kasar Belarus.
An haife shi a ranar 8 ga watan Yulin 1985 kuma ya fara aikin dan sanda a shekarar 2008.
Hedikwatar tsaron ta ce ta samu damar kai harin ne sakamakon wasu bayanan sirri da ta samu kan katafaren sansanin na kungiyar Ansaru, wadda ta balle daga kungiyar Boko Haram.
Samamen na hadin gwiwa ne tsakanin rundunonin ‘yan sanda masu yaki da manyan laifuka karkashin jagorancin Operation Puff Adder, a cewar rundunar.