Uwa ta jefa ’yarta mai shekara 3 a kejin dabbobi a gidan zoo

Uwa ta jefa ’yarta mai shekara 3 a kejin dabbobi a gidan zoo

Uwa ta jefa ’yarta mai shekara 3 a kejin dabbobi a gidan zoo

An kama wata uwa bayan ta jefa wata ’yar shekara uku a cikin kejin dabbar bear da ke gidan namun daji.

Masu gadi da ’yan kallo suna kallo cikin firgici yayin da babbar dabbar ta tafi kan yarinyar amma ba ta kai mata hari ba.

Dabbar Bear – mai suna Zuzu – ta matsa kusa da yarinyar, amma sai ta wuce, cikin sauri ta shige wani bangare na kejin, sai ma’aikatan suka ceto yarinyar, inji wasu shaidu.

A yanzu mahaifiyar yarinyar tana fuskantar tuhumar yunkurin kisan kai da yin ganganci da rayuwar yarinyar.

Wadansu da ke wurin sun yi kokarin hana ta jefa yarinyar a kejin, kamar yadda kakakin gidan namun dajin da ke Tashkent a kasar Uzbekistan da ke tsakiyar Nahiyar Asiya ya sanar.

Kakakin ya ce: “Wata mata ta jefa wata karamar yarinya cikin rukunin dabbobin bear da aka killace, a gaban wajen da baki ke tsayawa.

“Ba a san cikakken dalilinta ba na aikata haka ba.

“Baki dayan ma’aikatan gidan namun dajin sun yi kokarin hana ta – amma sun kasa.”

Ta ce: “Muna jin tsoron ko tunanin hakan zai yi sanadin rasa ran yarinyar, in da dabbar ta kai farmaki ga yarinyar.”

An tsare mahaifiyar wacce ba a bayyana sunanta ba – kuma tana fuskantar hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari, inji rahotanni.

Yarinyar ta samu rauni a kanta bayan faduwarta a cikin kejin, “Amma babu alamar rauni da dabbar ta yi mata,” inji ta. (dailyrecord. co.uk).