Yi wa Su Dariye Afuwa Abu Ne Mai Sanyaya Guiwa —Lauyan EFCC
Alamomi sun nuna shi ma shugaba Buhari haka zai bar mulkin bai magance matsalar cin hanci da rashawa ba
Rotimi Jocobs lauya ne ga Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) kuma wanda ya shigar da kara a kan tsofaffin gwamnoni hudu da hukumar ta daure; Margayi Diepreye Alamieseigha na Jihar Bayelsa, Joshua Dariye na Filato, Jolly Nyame na Taraba da kuma Orji Uzo Kalu na Jihar Abia wanda daga bisani Kotun Koli ta soke hukuncin durin da aka yi mishi.
Aminiya ta yi wata hira da Rotimi Jacobs, inda ya yi magana a kan afuwar da shugaban kasa ya yi tsofaffin gwamnonin da wasu abubuwa.
- NAJERIYA A YAU: Abin da Ya Sa Aka Yafe wa Dariye Da Jolly Nyame
- Matasan Kirista sun saya wa masallaci sabon janareta a Filato
Ku biyo mu:
Wasu lauyoyi na ganin afuwar da aka yi wa su Dariye ya saba wa doka, shin me za ka ce?
Idan ka duba sashe na 175 na Kunding Tsarin Mulkin Najeriya, ba za ka ce an yi abun da ya sabawa doka ba.
Sai dai kuma, sashe na 15 ya ce dole ne kasa ta yi mai yiwuwa domin kawar da almundahana, don haka idan har za a binciki mutum kuma a same shi da laifi, to bai kamata a ce a sake shi ba, don kuwa ya saba sashe na 15 kuma zai zama tamkar ana kara karfafa cin hanci da rashawa ne.
Duk da cewa suna kokarin aiki da sashe na 175, akwai bukatar a bi matakai kafin a iya yi wa mutum afuwa.
Da ma Dariye a kasar Ingila ne aka fara gurfanar da shi bayan da aka kama shi a otel tare da tsabar kudi masu yawan gaske a dakinsa, yana wadaka da kudaden ya rarraba wa abokansa da ’yan matansa.
Daga baya dai aka ba da belin shi ya dawo Najeriya, bayan samun rahoto da Ingila ta turo a wancan lokacin Shugaban Kasa Obasanjo, shi kuma ya tura shari’ar ga Babban Lauyan Gwamti da kuma EFCC domin gurfanar da shi a gaban kotu.
Bayan dogo bincike da hukumomin Ingila suka gudanar sai suka gane cewa Dariyen yana da kadarori a kasar.
Shi dai ana tuhumar shi ne da ruf da ciki a kan kudi Naira Bilyan 2.1 da ma wasu kudade da ya yi awon gaba da su ta wani asusun bogi da ya bude.
Bayan gudanar da bincike da gwamnatin Najeriya ta yi kuma ta same shi da laifin da ake tuhumar shi, wannan ne ya sa a shekara ta 2018 kotu ta yanke mishi hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari.
Yanzu kuma, afuwar da aka yi mishi tamkar an wanke shi ne daga laifin da ya aikata tare da mayar mishi da kadarorin da aka kwace daga hannunsa.
Shin kana ganin za a iya komawa kotu domin sake kwato kadarorinsa da aka kwace bayan wanke shi da dukkanin laifukan da ya aikata?
Kasar Birtaniya sayar da kadarorinsa ta yi kuma ta turo kudaden ga gwamnatin Najeriya, wadda ita kuma ta tura kudaden ga gwamnatin Jihar Filato.
Yanzu kuma mu a Najeriya ba za mu iya yin abun da Birtaniya ta yi ba, kuma bai kamata a sake shi ba, ba tare da an tambayi sauran hukumomi ba ko akwai wata kara da aka shigar a kansa.
Ka ga yanzu ko mun je kotu ba wata hujja da za mu iya gabatarwa a gaban kotu domin an riga da an yi masa afuwa.
Matsalar ma a yanzu ita ce zai iya fitowa takara, zai iya komawa Sanata.
Wannan mutumin fa an daure shi a 2018, a lokacin yana Sanata mai ci kuma ana biyan shi duk wani alawus din da sauran sanatoci ke karba alhali yana gidan yari — to kaga ke nan ba yaki mu ke da cin hanci da rashawa.
Sauran tsofaffin gwamnonin da aka daure kuma sun mayar da gidan yari tamkar wuraren shakatawa da jin dadi, sannan duk wasu magoya bayansu masu wata bukata a wajensu dole sai sun je gidan yarin sun biya su kafin su biya musu bukatunsu.
To ta yaya za ka yi wa irin wadannan mutanen afuwa ba tare da sun shiryu ba?
Mene ne illar irin wannan afuwar?
Da yawa daga cikin alkalai gwiwarsu ta yi sanyi saboda idan aka duba za ka ga alkalan ba sa wani wahalar da kansu wajen daure wadanda ake tuhuma saboda sun san cewa daga baya gwamnati na iya sakin su.
A loakacin cutar COVID-19 an nemi shugaban kasa da ya yi wa mutane dubu 2,500 afuwa don gudun yaduwar cutar.
A 2011 lokacin da aka yi zanga-zanga, EFCC ta kama tare da daure mutane da dama da aka same su da hannu a badakalar tallafin man fetur, wanda ni kaina na taimaka wajen daure mutane goma daga cikinsu.
Amma yanzu su wadancan mutane suna cikin wadanda aka yi wa afuwa a lokacin COVID-19 domin yanzu haka suna nan suna gudanar da rayuwarsu a cikin al’umma.
Idan ana yin haka ta yaya ka ke ganin za a iya kawo gyara a cikin al’umma, alhali ba a hukunta masu aikata laifi?
Alal misali, Shari’ar Orji Uzor Kalu. Na san an yi wa Mai Shari’a Idris da ke sauraran shari’ar karin girma, amma Orji Kalu da wani kwamishinansa da wani kamfani suka bukaci Shugaban Kotun Daukaka Kara ya bari Mai Shari’a Idris ya dawo ya yanke hukunci.
Daga baya su wadannan mutane da suka bukaci ya dawo suka sake komawa kotu suna kalubalantar dawowar tasa, cewa ba daidai ba ne.
Daga karshe, duk shari’ar da aka yi da shi tun a 2007 ta zama a banza.
Yaznu kuma da muka nuna musu ba mu gaji ba, sai suka dauke shari’ar daga Legas zuwa Abuja ba tare da tuntubar kowa ba, sannan kotu ta ce ba za mu iya sake gurfanar da shi ba.
Ka ga irin wannan abubuwan suna karya guiwa; Idan har mun san ba za mu yi yaki da rashawa ba kawai mu fada, kowa ya je ya yi abun da ya ga dama.
Marigayi Alamieseigha shi ne tsohon gwamnan na farko da na gurfanar a gaban kotu.
Gurfanar da gwamna ba karamin aiki ba ne, haka ma gudanar da bincike a kansa, saboda ba kowane alkali ba ne yake da kwarin guiwar iya yanke wa tsohon gwamna hukunci.
Za ka iya shigar da kara, sai dai samun shaidu shi ke da matukar wahala saboda mafi yawan shaidun duk mutanensa ne da ba za su iya juya mishi baya ba.
Don haka yana da matukar wahala, ni kadai na san irin wahalar da na sha a lokacin da aka yi shari’ar gwamnonin nan uku, Alamieseigha, Dariye da Nyame.
Shi ma Kalu da shi ne zai kasance na farko inda ba a yi watsi da kararsa ba, kuma har yanzu ba maganar Naira Bilyan 7 mallakin jihar Abia da aka salwantar da su.
Duba da irin abun da ya faru, shin kana ganin a rufe hukumar EFCC ke nan?
Rufe hukumar ba zai yi maganin matsalar ba, sai dai ma ya haifar da karin matsaloli.
Saboda har yanzu hukumar tana iya nata kokari; Baya ga gurfanar da masu cin hanci da rashawa, hukumar na kama matasa masu damfarar mutane ta kafofin sadarwa na zamani, wadanda su kuma rashin aikin yi ne ya jefa su cikin wannan harkar.
Shin ko akwai nau’o’in afuwa?
Eh akwai nau’o’in afuwa.
Akwai afuwar da za a yi wa mutum wadda ba ta shafi kadarorinsa ba ko kuma tarar da kotu ta yi mishi.
Amma afuwa wacce aka wanke mutum mai laifi ita ce ke lalata komai a shari’ar da ake yi.
A tunaninka wane bangare ne ke da matsala?
Cin hanci ne ya yi mana katutu. A tunanina lokacin da aka zabi shugaban kasa mai ci a yanzu, idan ya hau zai magance matsalar ta cin hanci da rashawa ko kuma ta rage domin a ciyar da kasar nan gaba.
Amma alamomi sun nuna shi ma shugaba Buhari haka zai bar mulkin bai magance wannan matsala ba, tunda a yanzu shekara daya kawai ya rage a wa’adin mulkinsa.