A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

Matasan nan da aka sako bayan tsare su a Gidan Yarin Kuje, sun bayyana irin bakar wahalar da suka sha da kuma yadda rayuwarsu ta kasance a gidan. Matasan sun tsinci kansu a gaidan yarin ne bisa zargin su da cin amanar kasa da yunkurin kifar da gwamnati da cin amanar kasa lokacin zanga-zangar da […]

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

Matasan nan da aka sako bayan tsare su a Gidan Yarin Kuje, sun bayyana irin bakar wahalar da suka sha da kuma yadda rayuwarsu ta kasance a gidan.

Matasan sun tsinci kansu a gaidan yarin ne bisa zargin su da cin amanar kasa da yunkurin kifar da gwamnati da cin amanar kasa lokacin zanga-zangar da ta karade Nijeriya, a watan Agusta.

A ranar 5 ga watan nan na Nuwamba kotu ta sallami matasan su sama da 100 ne bayan Gwamnatin Tarayya ta janye zargin bisa umarnin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Sun bayyana wa Aminiya yadda aka kama su da irin baƙar wahalar da suka sha daga a hannun ’yan sanda da kuma Gidan Yarin Kuje.

Wahalar da muka sha a tsare

Ɗaya daga cikin matasan mai suna Fahad Ibrahim ya bayyana yadda ya tsinci kansa yana kwana a kofar bandakin Gidan Yarin Kuje, duk kuwa da tsananin doyin bayin.

Fahad ya shaida wa Aminiya cewa ce karamin yaro dan shekara biyu zai iya cinye ukun abincin da ake ba su a gidan yarin, ba tare da ya koshi ba. A hakan ma, abincin babu gishiri balantana dadi, amma dole suke ci, don su rayu.

Wani abokinsa da aka sako su tare ya ce sun shafe kusan kwana 70 babu abincin da ake ba su in bada garin kwaki da wake.

Fahad ya ce idan sun kamu da rashin lafiya kuma, ba a yin gwaji sannan babu magani a asibitin gidan yarin, in banda Paracetamol, sai dai su da ake tsare da su su saya da aljihunsu.

Matashin, wanda mazaunin unguwar Kabala Doki da ke Jihar Kaduna ne, yana daga cikin matasan da aka sako daga Gidan Yarin Kuje.

Matasa 39 ciki har da kananan yara biyu ’yan Jihar Kaduna ne aka sako daga cikin masu zanga-zangar, bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban kasan ya bayar da umarnin sakin samarin da aka kama jihohin Kano da Kaduna ne bayan bidiyon yadda wasunsu suka rika yanke jiki suna faduwa a kotu a Abuja, saboda yunwa a lokacin da ake gurfanar da su, ya karade kafofin sada zumunta.

Bullar bidiyon ta janyo kakkausar suka da Allah-wadai ga gwamnati, musamman ma ’yan sanda bisa rashin kula da matasan, wadanda akasarinsu yara ne ’yan kasa da shekara 18.

A zantawar wasunsu da Aminiya bayan sun shaki iskar ’yanci sun bayyana mata yadda aka kama su da kuma yadda rayuwarsu ta kasance a lokacin da suke tsare a kurkuku.

An saki ’ya’yan masu kuɗi —Fahad

Fahad ya ce a ranar zanga-zangar aka kama shi a kusa da gidan yari da ke Kaduna. Ya ce bayan an kai su ofishin ’yan sanda sai aka zabi wasu daga cikinsu wadanda iyayensu ke da hali, aka bayar da belinsu.

“Mu kuma sai aka wuce da mu Abuja. A ofishin ’yan sanda da ke Abuja (FCID) sau daya ake bayar da abinci a kullum.

“Daga nan sai aka kai mu Gidan Yarin da ke Kuje. A nan kuma abincin da suke bayarwa ko yaro ɗan shekara biyu zai cinye ukunsa bai koshi ba. Toh ina ga babba?”

Mu ke saya wa kanmu magani

Fahad ya ce haka suka ci gaba da hakuri da zagi da duka, duk da cewa shi ba a buge shi ba, amma ya ga yadda ake dukan wasu daga cikinsu.

Ya kara da cewa, “da an yi Sallar La’asar ake son kowa ya koma daki, wanda bai koma da wuri ba ne ake duka a gidan yarin.

“Sannan babu magani a asibitinsu domin Paracetamol kaɗai suke bai wa mutum ko kuma a ce ya ba da kudi a siyo masa.

“Na yi zazzabi amma ko na je sai dai kurum a ba ni Paracetamol, ba su yin gwaji kwayar paracetamol za su ba ka.
Kwana a kofar bankaki.

“A cikin daki mu 37 ne, saboda cinkoso ni a bakin bayi nake kwanciya, ga wari na fitowa daga bayin.
“Kwanciya a matse ake, ga kuma zafi ga sauro. A gidan Yari suna ba da abinci ne sai uku.

Abinci: Ci kar ka mutu

“Wake da safe sannan kuma sai shinkafa, wanda yaro zai iya cinye ’yar kwanon guda uku bai ƙoshi ba, shi za a bai wa babba.

“Sannan da yamma sai a ba da tuwo, shi ma tuwon dai ga yadda yake. Ga miya babu gishiri ko magi kuma babu dadi amma haka muke ci saboda kada mu zauna da yunwa.

“Dole ka ci domin idan ba ka ci ba ba ka da wani abinci, sai dai muka yi ta hakuri da rokon Allah Ya kawo mana sauki.

“Saboda haka ba na barci kowane lokaci, rokon Allah muke yi, Ya daura mu a kansu mu bar gidan.”

Fahad ya ce, “Addu’ar iyayenmu da tamu ce ta fito da mu. Abin dai babu daɗi musamman idan na tuna da mutanen gida, sai in ji babu dadi saboda sai in rinka tunani kawai ni kadai.”

Yunwa ta galabaita mu —Umar

Shi kuma Umar Yakubu, wanda aka sako tare da Fahad, cewa ya yi an zalunce su, sai dai Allah Ya bi masu hakkinsu.

Umar ya ce akasarin yara da aka tsare su tare sun wahala matuka saboda yunwa, wanda hakan ne ya sanya suka rika yanke jiki suna faduwa a ranar da aka kai su kotu.

“Gaskiya yara kananan sun wahala domin yaeda suka rika faduwa saboda yunwa a kotu, hakan ya tayar wa da kowa hankali har alkalin ya bukaci a ba su abinci. Suna ci kamar ba su taba ganin abinci ba.

Mu kuma muna kallo muna kuka saboda halin da muke ciki,” in ji shi.

Ya kuma mika godiyarsa ga ’yan uwa da iyayen da suka taya su da addu’a har suka samu fitowa daga kurkuku.
Kwananmu 70 muna cin garin kwaki

Shi ma Hassan Muhammad mazaunin Unguwar Malali, wanda aka sako su tare ya bayyana zamansu a Gidan Yarin kuje a matsayin mara dadi.

Ya ce, “An kama ni ne a ranar 5 ga watan Augusta 2024, a kan Titin Ahmadu Bello a lokacin zanga-zangar yunwa a Kaduna.

“Bayan kama mu da aka yi, sai suka kai mu sashen binciken masu aikata manyan laifuka na CID a Kaduna inda aka dauki bayananmu kafin aka wuce da mu Abuja (FCID).

“Mun yi kwana 18 a FCID kafin suka kai mu Gidan Yarin Kuje. A Kuje muka yi kwanaki 68.

“Yanayin babu dadi sannan babu abinci mai kyau. Wake kurum da gari ake ba mu a kwanakin da muka yi a Kuje,” in ji shi.

‘Na yi zanga-zangar karshe’

Shi kuma Muhammad Abubakar daga Zariya cewa ya yi, “Mun koyi darasi tun bayan kama mu da aka yi, kuma ba za mu taba mancewa da abin da ya faru da mu ba har iya rayuwarmu.

“Ni dai ba zan sake shiga zanga zanga ba,” in ji matashin.

Ku zama mutanen kirki -Kwamishina

Bayan sakin matasan, Kwamishinar Jin Daɗi da Ci-gaban Al’umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu, ta shawarce su da su koma cikin al’umma su cigaba da zama mutanen kirki masu yada zaman lafiya a duk inda suke.

Ta kuma ce akalla masu zanga-zanga 39 manya ne sai Yara biyu aka Sako a jihar kuma za’a kuma duba lafiyarsu tare da basu tallafi da ya dace a gwamnatance.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta