A 2015 kuri’un al’ummar Yamaltu Deba duk na dankwambo ne – Aliyu Zagi

Shugaban karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe Alhaji Dauda Aliyu Zagi, ya ce sakamakon ayyukan madalla da Gwamna Ibrahim Hassan dankwamo ya yi musu a yankin musamman hanyar Kanawa zuwa Jauro Gotel ta Jihar Adamawa, ta sa bai zai samu adawa ba a zaben shekarar 2015.Alhaji Dauda Zagi, ya bayyana hakan ne a lokacin […]

A 2015 kuri’un al’ummar Yamaltu Deba duk na dankwambo ne – Aliyu Zagi
A 2015 kuri’un al’ummar Yamaltu Deba duk na dankwambo ne – Aliyu Zagi

Shugaban karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe Alhaji Dauda Aliyu Zagi, ya ce sakamakon ayyukan madalla da Gwamna Ibrahim Hassan dankwamo ya yi musu a yankin musamman hanyar Kanawa zuwa Jauro Gotel ta Jihar Adamawa, ta sa bai zai samu adawa ba a zaben shekarar 2015.
Alhaji Dauda Zagi, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Sakatariyar karamar Hukumar, inda ya ce, “A baya kafin yin hanyar idan ka ce mai mota ya kai ka Deba sai ranku duka ya baci dalili shi ne hanya ce da ba ta wuce tafiyar minti talatin ba amma sai kun yi awa biyu.”
Alhaji Dauda Zagi, ya ce al’ummar karamar hukumar sun shafe fiye da shekara 29 suna neman a yi musu hanyar ba su samu ba sai a lokacin Gwamnan da yake aiki don talaka wato dankwambo.
Shugaban ya ce a dalilin hanyar kauyuka da dama a yankin sun fara cin moriyarta a bana ta hanyar fitar da amfanin gona zuwa cikin sauki. “Garuruwan da suka ci moriyar hanyar sun hada da Zamfarawa da Deba da Mararrabar Kuri da kuran Mota da Lano da Jagali da Dasa da Dumbu da Kurjale zuwa Jauro Gotel iyakar Gombe da Adamawa,” inji shi.
Game da yin gada a garin Kuri kuwa da gwamnatocin da suka shude suka gagara sai a gwamnatin dankwambo ya ce gina gadar kadai da hanyar Deba suka sa ya zama ba su da wani dan takara a zaben shekarar 2015 sai Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo. “Ina tabbatar wa Gwamna dankwambo idan lokacin siyasa ya yi kada ya zo Yamaltu Deba domin mun ajiye kuri’unmu dominsa, ina kira ga jam’iyyun adawa cewa kada su bata wa kansu lokacin zuwa su yi mana kamfe domin babu wata kofa da za ta sa su bar dankwambo ya kubuce mana,” inji shi.