A Abuja da Legas muka kashe kudin rarar mai – Babangida

Tsohon Shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Ibrahim Badamsi Babangida ya bayyana gwamnatinsa da waliyiya idan aka kwatanta da gwamnatocin da suka biyo bayanta idan ana maganar almundahana ne. Janar Babangida wan da ya bayyana haka a tattaunawa da Mujallar Zero Tolerance da Hukumar Yaki da yinwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta watan Disamban 2014, lokacin […]

A Abuja da Legas muka kashe kudin rarar mai – Babangida
A Abuja da Legas muka kashe kudin rarar mai – Babangida

Tsohon Shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Ibrahim Badamsi Babangida ya bayyana gwamnatinsa da waliyiya idan aka kwatanta da gwamnatocin da suka biyo bayanta idan ana maganar almundahana ne.

Janar Babangida wan da ya bayyana haka a tattaunawa da Mujallar Zero Tolerance da Hukumar Yaki da yinwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta watan Disamban 2014, lokacin da yake amsa tambaya kan cewa gwamnatinsa ce ta halatta almundahana ya ce, “Eh na sani, ina iya yarda da haka, to amma duk wanda zai yi adalci ba shi da zabi face ya kira mu waliyayai. Ina jin gwamnatina ta gano wasu wuraren da ake almundahana kuma ta magance su.”
Ya kara da cewa “Ba ni da hujjoji a hannu, amma idan abin da nake karantawa a jaridu, shi ne abin da yake faruwa, to ina jin mu waliyai ne. A shekara ina samun kasa da Naira biliyan bakwai daga kudin mai, a cikin shekara daya yanzu gwamnatoci na samun Dala biliyan 200 zuwa 300, amma ba a samu ci gaban da ya kamata ba.”
Janar Babangida ya ce Dala biliyan 12 na rarar man fetur da aka samu lokacin Yakin Tekun Fasha bas ace su aka yi ba, maimakon haka an yi amfani da su ne wajen yin gine-gine kamar gina Abuja da gada ta uku da ke Mailand a Legas.
“Na gina Abuja. Yau muna dsa abon birnin Tarayya, a na muka yi amfani da kudin. Na yi muku gada ta uku a Mailand da ke Legas, yanzu ba z aka iya gina irinta ba duki da dimbin kudin da Najeriya take samu. Nawa ta ci min, Dala miliyan 500 ko 600 ko 700,” inji shi.
Da aka tambaye shi inda yake samun kudi, sai ya ce yana daya daga cikin wadanda suka fi jari a wani bankin Najeriya da bai fada ba. Ya ce, “Bari in gaya muku, ni ne Shugaban kasar da aka fi bincika a Najeriya. Ya kamata zuwa yanzu wani ya fito ya ce ga abin da ya gano. Duk gwamnatin da ta zo a bayana ta bincike ni saboda wannan tunani, domin suna so su kwato biliyoyin Naira da na sace. Idan ba so kake ka nun aba ka iya bincike ba, ya kamata ka gano wani abu, in kuma a’a wannan matsalarka ce.”
Da aka tambaye shi me ya sa mafi yawan shugabannin Najeriya suke kudancewa fiye da lokacin da suka hau mulki, sai ya ce, “Ka ce mafi yawa, bari in gaya maka game da ni. Lokacin da nah au mulki a watan Agustan 19985, na yi rantsuwar bayyana kadarorina abin da na mallaka yana nan a rubuce, kuma na sauk ba wani canji mai yawa. Kafin in zama Shugaban kasa ina zaune a wannan muhalli ga alama mutane sun manta ne.”
Game da rage darajar Naira Babangida ya ce, gwamnatinsa ta so yin gasa a fannin tattalin arziki da sauran kasasshen duniya a lokaci, “Amma mun yi kokarin ganin Dal aba ta wuce Naira 22 ba, lokacin da na sauka ta haura zuwa Naira 85. Abacha gwarzo ne ya yi kokarin tsayar da ita a tsakanin Naira 85 zuwa 90.”

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista