A agaza wa mutanen Gaza
A yau tsaro a duk fadin duniya ya yi kamari, inda har an kai ana yaki tsakanin masu duwatsu da jiragen sama! Kuma duniya ta kauda kai. Isra’ila na yin kissan kare dangi, tabbas lokaci ya yi da za a kai wa mutanen Gaza agaji.Isra’ila ta dunfari mutane da boma-bomai masu ‘ya’ya, inda take kashe […]
A yau tsaro a duk fadin duniya ya yi kamari, inda har an kai ana yaki tsakanin masu duwatsu da jiragen sama! Kuma duniya ta kauda kai. Isra’ila na yin kissan kare dangi, tabbas lokaci ya yi da za a kai wa mutanen Gaza agaji.
Isra’ila ta dunfari mutane da boma-bomai masu ‘ya’ya, inda take kashe na kashewa! Bom bai san yaro ko tsoho ba, yayin da mutane ke gudu da karfin kafafuwansu, ba matashi, ba maza ko mata ko yara kowa na ta kansa tun kafin ranar! Wasu na ganin ko a busa kahon!
Bala’in ya zama bala’i! kasar da aka yi jihadi don daukaka Kalmar Allah! Ta yaya za a kwace ta a wannan zamanin? Hakika a yau duk masu neman shahadar gaske sai su wuce Gaza, su kai agaji. Halin da ake ciki mutane da dama basu ga murnar fita daga watan Ramadan ba!
Larabawa sun zama ‘yan gudun hijira a kasashensu, sannan a kasashe makwafta an kange Palisdinawa daga shiga iyakokin! Abin sai Innalillahi Wa Ina Iallahi Raji’un. Mutane sun zama kauyawa ba ruwa ba wuta, sun koma kwana a ramuka don su rayu, su ga hasken ranar gobe!
Ana sahur cikin zulumi, ana shan ruwa cikin zulumi, an ruguza gidajen abinci, asibitoci, kasuwa da makarantu, ina za ku wurga kanku? Kowa ya sani zalunci ba ya dauwamma. kasashen da ake kashe Musulmi da yaki da Musulunci sun wuce Gaza da Irak da Pakistan da Nijeriya da Siriya, a kusan kowace kasa ana wannan zagon kasan na ganin an kawo karshen Musulmi, amma ba zai yiwu ba, Allah zai daukaka Musulunci.
Sulhu ta hanyar yarjejeniyar zaman lafiya ya faskara, inda kasashen Larabawa da wadanda Musulmi suka fi yawa ba abin da suke yi sai magana da fatar baki! Yayin da Amurka ta tsaya kan cewa Isra’ila na da ‘yancin kare kanta! A daidai lokacin da kasashen da suka shigo tsakani
na fama da matsalolin da suka shafi kansu kamar Masar, inda a halin yanzu tana fama da matsalolin cikin gida, musamman a fagen siyasa, tabarbarewar tattalin arziki da tawaye daga ‘yan ta’adda.
Idan ma dimokuradiyyar gaskiya ce a bar Hamas da karfin iko mana, me zai sa a sirka da Fatah a sunan daidaita ikon zartarwa, wannan munafuncin na Amurka zai koma kanta, kuma a kwana a tashi wata rana Yahudawa za su gudu daga Isra’ila, alkawalin Allah gaskiya ne!
Yayin da a Nijeriya Barno da Yobe sun zama kango saboda yake-yake, an gaza kubuta da ‘yan mata, shugabanni da malamai matsorata! Iskar ta karkato Kano, wadda ta zama kamar kwalin ashana, bom ya zama kamar buga banga. Hakan yasa manazarta da dama ke zargin hannun gwamnati, domin abin da kamar wuya a dade ana yi sai gaskiya, don idan an gaza samun mafita a sauka a kafa sababbin shugabannin da za su kai mu tudun tsira. Idan ba hannun jami’an tsaro, ta yaya za a kai bom caji ofis ko a inda ‘yan sanda da sojoji suka killace, sai ya tashi su taho da
karfi kamar za su yi wani abin a zo a gani! Ana kama wadanda ake zargi, amma har yau ba wanda aka gurfanar, balle yanke hukunci, kuma an hada kai tsakanin alkalai Musulmi da wadanda ba Musulmi ba ana cutar da al’umma.
Lallai hare-haren da Isra’ilakaiwa a Gaza sun yi muni, domin ta’addancin ya fito fili. Kuma ana muzahara a ko’ina, me zai hana mu fito a nan Nijeriya, mu tafi Abuja don nuna wa duniya bakin cikinmu. Halin da ake ciki ya wuce wai yaki da ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayin jaddada addini, domin da gwamnati da gaske take da an sha kan lamarin. Mu daga nan Nijeriya ba abin da za mu yi sai dai mu agaza wa mutanen Gaza da addu’o’i kamar yadda muke yi wa kasarmu da kawunanmu.
Buhari Daure
Muryar Talaka
[email protected]