A arce wa bashi

A sabuwar shekara miladiyya ta dubu karamin Lauje da sili da tsayuiwa bisa kafa daya, masana tsarin tsimi da tanadi sun gargadin al’umma kan lallai mu yunkura, mu arce daga tafarkin tsimi da ta’adi.  Don haka Farfesun Rabon sulalla, wanda muka taba bayar da labarinsa a shekarar da ta arcek, ya ce babbar shawarar da […]

A arce wa bashi

A sabuwar shekara miladiyya ta dubu karamin Lauje da sili da tsayuiwa bisa kafa daya, masana tsarin tsimi da tanadi sun gargadin al’umma kan lallai mu yunkura, mu arce daga tafarkin tsimi da ta’adi.  Don haka Farfesun Rabon sulalla, wanda muka taba bayar da labarinsa a shekarar da ta arcek, ya ce babbar shawarar da zai bai wa al’ummar duniya, ita ce kowa ya yi yunkurin arce wa bashi. Wadanda suka fasko manufarmu da sun ari faden Malam Tunau, sais u yin a jaki, don kada su ci na jaki.
Yan makaranta, kundin labaran da, da na yanzu, ya tabbatar kasar Haurobiya, wadda Turawan mulkin mulak’u suka hade Sashen Kadawa da Arewatawa, tun a shekara ta dubu da man uniyar sama da sili da tsayuwa bisa kafa daya, don Shugaba Jatau Mai Gudun-loko, gwamantinsa za ta gudanar da gagarumin ruguntsumin biki. To ko murnar me Haurobiyawa za su yi, alhali a ana bin su bashi? Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya, ku sani cewa Shagabannin Haurobiya ciwo bashin kunya, suka jefar da ita a kwarin kunya; sun ciwo bashin tarwatsa mabambatan kabilun kasar nan, don haka ake ta yin tsare-tsaren dakan daka shikara daka, tankaden bakin gado. Uwa – uba sun yi bashin camamawa da kwashi-kwaraf, shi yasa suka kware a samartakar kusu.
Kada mutum ya ga galala, ya dinka galila. Kowaya yi fafutikar neman sila wadda ta fi salsala da salala. Mu yi n jaki, don kada mu ci na jaki; ban da juyin wainar matar manomi.
Kada dai in cika ku da surutu rututu kamar aku kuturu, ko Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters. Batu na ingarmabn karfen karafa. Shekara dari sili da Haurobiya ta yi a matsayin dunkulalliyar kasa, ta yi su ne cikin nuna gazawa, musamman tabarbarewa tsare-tsaren tsimi da tanadi, inda muka samu gwanayen tsimi da ta’adi suna ta wadaka, alhali gama-garin mutane na fama da talalar talauci.
Mu biya bashi, shi ne matakin farko. Don haka nike bai wa Gwamnatin Haurobiya shawara, kada ta sake ta salwantar da dukiyar al’umma wajen kade-kade da bushe-bushen bushasha. Abin da kawai ya fi dacewa, mu cefanar da gwanayen kwashi-kwaraf, mu biya lamuninmu. Wadannan gwanaye dai kowa ya san sun hada da Baudadden Joji da Santala kwaiduwa da Farfesun Gareji da Uwargida Mai dama fate-fate da Aminin-dabo da Sisiliya, wadda ta sulale da sulalla. Ko nawa kasar Haurobiya ta cefanar da wadannan miyagu tabbas za ta biya basussukan da suka yi mata dabaibayi.
Hanya mafi sauki wajen wanbcakalar da masu kwashi-kwaraf, ita ce, al’umma ta daina sha’awarsu; a daina ba su damar jan ragamar al’umma; mutane su zama masu ta –ido, ka da mutum ya fetsare ya rarike lalitar al’umma, ya zo yana yi musu fankama, babu tsoron Mai-duka.
Akwai masu zuki-ta-malle, kama kare ka hada shi da zomo, su ma gungunsu daban, sun kuma hada da Gaulan Jatau, da ke bas hi shawara kan harkokin dama-dama da kurda-kurdar wasan Samson-siya-siya da kwakwalen al’umma; sai Rubabben Abban-titi, shi mai bayar da shawara ne a kan harkokin watsattsake a mujallu da mukalu da kwakwazo a akwatin magana da mai hoto; sai Karen farmaki In-kwafe.
Dole sai mun yi watsi da miyagun dabi’unmu, mun tattaro kyawawan ta’adu, mun nunnunka su. Mun rarraba a tsakanin al’umma, sannan Haurobiya za ta samu masalahar rayuwa cikin kananan shekaru ba sai an kai shekara dari sili ba. Dom haka ba biki ya kamata mu yi, hasali ma kamata ya yi mu yi makokin rashin jagororin da suka yi fafutikar dora kasar nan da al’ummarta kan turba ta gari; mu kuma ga wallen wadanda suka jefa mu cikin garari.
Mu daina ciwo bashin miyagun dabi’u, mu daina ranko da kyawawan ta’adu. Wannan ita ce mafita, musamman in mun yi la’akari da cewa Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta kasa kaimu gaci. Wajibi ne mu yi yunkurin jirkiceta; a yi juyin juya hali koda a tandar masa ne. to kun ji! Lallai wannan ya zama shi ne kuduri da salon shiga sabuwar shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya. Kowa ya arce wa bashin miyagun ta’adu.