A azumin bana gero da wake ba su samu kasuwa ba a Sakkwato
Buhunan gero da wake ga sunan tsibi-tsibi a kasuwa wurin manya da kananan ‘yan kasuwa duk da shigowar watan azumin Ramadan, abin da wasu ke ganin karancin masayan yana da nasaba da rashin biyan albashin ma’aikatan Jihar Sakkwato cikin lokaci. Ana bukatar Wake saboda yin Kosai, Gero kuwa don yin kunu da koko a wasu […]
Buhunan gero da wake ga sunan tsibi-tsibi a kasuwa wurin manya da kananan ‘yan kasuwa duk da shigowar watan azumin Ramadan, abin da wasu ke ganin karancin masayan yana da nasaba da rashin biyan albashin ma’aikatan Jihar Sakkwato cikin lokaci.
Ana bukatar Wake saboda yin Kosai, Gero kuwa don yin kunu da koko a wasu bangarorin arewacin Najeriya a kullum cikin watan azumi hakan ya sanya manoma ke kawo albarkatun a kasuwa sosai cikin watan.
“Akwai su gero da wake da yawa a kauyuka da biranenmu” a cewar wani mai sayarda gero a tsohuwar Kasuwar Sakkwato Alhaji Amadu.
Alhaji Ahmadu wanda ke sana’ar sayar da gero tun shekarar 1980 ya ce “Buhun gero har yanzu yana nan kan dubu 10 zuwa 11,500 kudin da muka saye shi a lokacin kaka (girbi).
“Shi kuma Wake muna sayan buhu kan farashin Naira dubu 20 mu ajiye shi a maboya tare da kayan da zai hana mashi lalacewa, amma yanzu farashin ya yi kasa ana samu kan 18,000 ko 15,000 ko 17,000 ya danganta da kalar waken da kake bukata.”
Babban dan kasuwar ya sha mamaki a wannan azumin, ya fara babu kasuwa kamar yadda ya yi tsammani.
Amadu bai zaci tun farko za a samu dagawar farshin gero ba, don haka yake kira ga mutane su ji tsoron Allah su daina karin da bai da tushe don su kuntatawa talakawa.
A kasuwar Kara wadda take rumbu ce ta gero ana samun buhun gero tsakanin Naira dubu 10 zuwa dubu 11. Wake kuma kanana ana samun su Naira dubu 13 zuwa dubu 14 kowane buhu. Haka kuma manya ana sayar da shi dubu 16 zuwa 17 kala-kala ne akwai har wanda ake sayarwa Naira dubu 19.
“Muna fuskantar rashin cinki sosai a wannan lokacin, tun da ka ganni ina shan inuwa karkashin itace, kasan babu ciniki, da akwai kasuwa, wane ni nan, in samu lokacin barci a yini daya.” Inji shi.
Dan kasuwar ya ta’allaka lamarin ga rashin baiwa harkokin noma muhimmanci da wannan gwamnati ta yi.
Yana iya tunawa duk kwana 10 na farkon azumin Ramadan gero da wake suna kara kudi, daga yadda aka saba, amma banda wannan shekarar.
Nuradden Sani shi ma babban dan kasuwar gero ne dake cikin babbar kasuwar Sakkwato ya ce farashin gero a wake har yanzu yana nan bai canja ba, buhu 12,000 in da ake sayar da mudu daya Naira 320.
A babbar kasuwar Sakkwato mai magana da yawun kungiyar masu sayar da gero, Malam Umaru Siniyo ya ce “Kafin watan azumi ma ya kama, sai na sayar da buhu 10 a yini guda, in rike kusan dubu 100, amma a wannan shekarar mun samu canjin kasuwa ba kamar yanda aka saba ba.”
Ya kara da cewar “A yau da nake magana da kai ban sayar da ko buhun wake guda ba, hana rantsuwa na sayar da buhu daya jiya. Buhun wake guda muna sayar da shi Naira dubu 20, Mudu kuma Naira 500, ga shi watan azumi muke ciki amma kasuwar ta kwanta, dole ta sanya muna sayar da buhu har 16,000, mudu kan 450.”
Mai magana da yawun kungiyar ya ce “Muna rokon Allah ya kawo mana canjin lokaci fiye da wanda muke ciki. Kwanan nan ne dai muka samu hukumar Zakka da Wakafi ta saye buhu 100 na shinkafa da alkama da wake kowannensu a daya daga ikin mambobinmu.”
Ya ce kungiyarsu tana da yawan mambobi sun fi dubu daya, domin tabbatar da ingancin kasuwanci a babban birnin jihar da kuma kananan hukumomi 23 na jihar Sakkwato.