A ba APC jan ragama a kowane mataki a ga aiki – baure

kungiyar Masu Kishin Jam’iyyar APC, (Forum for the Patriotic Members- FPM) ta bukaci al’ummar Najeriya su ba jam’iyyar damar kafa gwamnati ta hanyar zaben ’yan takararta tun daga matakin kansila zuwa Shugaban kasa domin samun kyakkyawan shugabanci da gudanar da ayyukan ci gaban kasa.Shugaban kungiyar Masu Kishin APC, Alhaji Lawal Abubakar baure ya bayyana haka […]

A ba APC jan ragama a kowane mataki a ga aiki – baure

Alhaji Lawal Abubakar Vaurekungiyar Masu Kishin Jam’iyyar APC, (Forum for the Patriotic Members- FPM) ta bukaci al’ummar Najeriya su ba jam’iyyar damar kafa gwamnati ta hanyar zaben ’yan takararta tun daga matakin kansila zuwa Shugaban kasa domin samun kyakkyawan shugabanci da gudanar da ayyukan ci gaban kasa.
Shugaban kungiyar Masu Kishin APC, Alhaji Lawal Abubakar baure ya bayyana haka lokacin da shi da Sakataren kungiyar, Musa O. Wakaso, suka ziyarci ofishin Aminiya a Abuja, inda ya ce sun samu amincewar jam’iyyar wajen yada manufofin kungiyar na kokarin ceto talakawan Najeriya daga mummunan halin da suka samu kansu bayan dawowar dimokuradiyya a kasar nan.
“Manufofin jam’iyyarmu su ne na kungiyarmu, don haka muke fafutikar ganin kowane dan Najeriya ya shiga Jam’iyyar APC, ya kuma bayar da gudunmawa wajen kawo sauyi, ta yadda za a inganta rayuwar al’umma; a kuma daina yi musu alkawuran ’yan siyasa, wadanda a karshe ake kasa cikawa,” inji baure.