A ba dankwambo goyon baya don ciyar da Gombe gaba – danmasanin Tumu

Wani dan siyasa a karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe Alhaji Sale Ahmad danmasanin Tumu, ya bayyana Gwamna Ibrahim dankwambo na jihar a matsayin gogaggen dan siyasa da ya dace da jagorancin al’umma. Alhaji Sale danmasani, ya bayyana haka ne a Gombe a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, inda ya ce duk […]

A ba dankwambo goyon baya don ciyar da Gombe gaba – danmasanin Tumu
A ba dankwambo goyon baya don ciyar da Gombe gaba – danmasanin Tumu

Wani dan siyasa a karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe Alhaji Sale Ahmad danmasanin Tumu, ya bayyana Gwamna Ibrahim dankwambo na jihar a matsayin gogaggen dan siyasa da ya dace da jagorancin al’umma.

Alhaji Sale danmasani, ya bayyana haka ne a Gombe a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, inda ya ce duk da an yi kururuwar canji a ko’ina a kasar nan amma ayyukan raya kasa da Gwamnan ya yiwa al’ummar jihar sun sa jama’arsa ganin dacewarsa ya ci gaba da ayyukan alherinsa.
“Gwamna Ibrahim dankwambo mutum ne mai dattaku da jama’a ke neman irinsa don raya al’umma da ciyar da jiha gaba. A cikin shekara hudu da ya yi yana Gwamna duk wanda ya zo Gombe zai san cewa ta canja,”inji shi.
Alhaji Sale Ahmad, wanda shi ne shugaban wata kungiya ta Talba A-Z ya ce sake zaben dankwambo karo na biyu zai ba shi damar kammala ayyukan alherin da ya faro wadanda suka kai fiye da kashi casa’in na kammalawa.
Sai ya yaba kan yadda Gwamnan ya ce ya yafe wa kowa da wanda ya zabe shi da wanda bai zabe shi ba, inda ya bukaci al’ummar jihar su ba Gwamnan goyon baya don sake ciyar da jihar gaba.