A ba INEC damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi — IPAC

Ɗantalle ya kuma yi kira da a gaggauta soke Hukumomin Zaɓe na jihohi.

A ba INEC damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi — IPAC

Majalisar Gabatar da Shawara a Tsakanin Jam’iyyu (IPAC) ta yi kira da a gaggauta yin gyara ga Kundin Tsarin Mulki da kuma Dokar Zaɓe domin bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) damar gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar nan.

Shugaban IPAC na ƙasa, Alhaji Yusuf Mamman Ɗantalle ne ya yi wannan kira a Abuja, yayin taron tuntuɓar juna karo na uku da jam’iyyun siyasa na 2024, wanda Hukumar Zaɓe ta ƙasa ke ɗaukar nauyin gudanarwa.

Majalisar ta kuma ƙi amincewa da ƙudirin dokar da Majalisar Dattawa ta gabatar na samar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙananan Hukumomi, inda ya ce idan aka yi la’akari da hakan, lamarin zai zama tamkar wata Hukumar Zaɓe ce ta jihohi (SIEC) a boye.

“Don haka ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma rashin tunani ne, sannan hakan zai kawo cikasa ga gudanar da zaɓe da kuma dimokuraɗiyyar.

“Hakazalika zai kasance almubazzaranci da dukiyar al’umma a daidai lokacin da al’ummar ƙasa ke fama da halin talauci da matsin rayuwa.”

Alhaji Mamman Ɗantalle ya kuma yi kira da a gaggauta soke Hukumomin Zaɓe na jihohi, inda ya zarge su da yin maguɗi a zaɓen ƙananan hukumomi a jihohi bisa umarnin gwamnonin jihohin.

Tun da farko, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, suna ci gaba da duk wasu shirye-shiryen domin gudanar da zaɓen Gwamnan Jihar Edo da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Satumba mai zuwa.