‘A ba sojoji hadin kai don su murkushe ta’addanci’

Sarkin Fawan Bonny Camp Alhaji Sallau Jibrin ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da ba sojojin Najeriya hadin kai tare da yi musu addu’o’i domin su samu nasara a yakin da suke yi da ’yan ta’adda a Arewa da Kudu.Sarkin Fawan ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da wakilanmu inda ya ce ya zauna […]

‘A ba sojoji hadin kai don su murkushe ta’addanci’
‘A ba sojoji hadin kai don su murkushe ta’addanci’

Sarkin Fawan Bonny Camp Alhaji Sallau Jibrin ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da ba sojojin Najeriya hadin kai tare da yi musu addu’o’i domin su samu nasara a yakin da suke yi da ’yan ta’adda a Arewa da Kudu.
Sarkin Fawan ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da wakilanmu inda ya ce ya zauna da sojoji a barikin Bonny Camp da ke Ikko, ya ce sojoji suna da aikin kishin kasa, kuma kishin kasa suka sa a gaba ba kabilanci ko nuna sani da sabo.
Ya kara da cewa bai dace ba wasu ’yan bindiga su nemi mai da kasar nan baya ba duk da arzikin da Allah Ya yi mata. “Abin kunya ne yadda wadansu da ba su son ganin an zauna lafiya, ga shi Allah Ya yi wa kasar nan arziki mai yawa,” inji shi.
Datiijon ya ce ya san Hafsan Hasfosin Sojan kasa Janar Tukur Yusuf  Buratai a matsayin soja tsayayye wanda da ikon Allha zai yi nasara a kan ’yan ta’addan da suka addabi kasar nan.
Alhaji Sallau Jibrin ya kuma bukaci mahauta su sanya gaskiya a gaba cikin sana’arsu ta fawa, inda ya ce cuta ba ta da kyau ga duk wanda yake son ya yi kakkyawar karshe. Sai ya hori matasa su dage ga yin ayyukan kwarai domin gudun abin kunya ga kai da kasa baki daya.