A bai wa mata jagorancin Nijeriya saboda maza sun gaza — PDP
Abin baƙin ciki ne yadda aka bar mata a baya duk da rawar da suke takawa wajen samar da sauyi a fagen siyasa.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta koka da yadda al’amura ke ci gaba da tabarbarewa a kasar, tana mai cewa tunda mazan sun gaza a ba mata dama.
PDP ta ce lokaci ya yi da ya kamata a bai wa mace damar jagorantar kasar, yayin da jam’iyyar ta koka kan halin da ƙasar ta tsinci kanta a ciki.
- An sauya wa ma’aikatan Kano lokutan aiki albarkacin watan Ramadana
- A gaggauta ceto ɗaliban da aka sace a Kaduna — Tinubu
Mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP, Ambasada Umar Damagum ne ya bayyana haka a yayin gabatar da jawabi a taron da Ofishin Shugaban Matan Jam’iyyar ya shirya albarkacin zagayowar Ranar Mata ta Duniya a yau Juma’a,
Damagum ya bayyana cewa, tun fil azal mata sun yi fice da nuna ƙwazo wajen sasanta rikice-rikice.
Mukaddashin shugaban na PDP wanda Sakataren jam’iyyar, Sanata Samuel Anyanwu ya wakilta, ya bayyana cewa, ba za a iya ƙayyade muhimmancin iyaye mata da matan ba.
Ya bayyana fatan cewa wata rana mace za ta zama shugabar Najeriya la’akari da yadda mazan suka gaza jagoranci.
“Wannan ne dalilin da ya sa mutanen da suka assasa jam’iyyar PDP suka fahimci muhimmancin mata.
“Abin da ya sa aka wayi gari jam’iyyar ta zama mafi riƙo da tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya da Afirka.
“Wannan ce jam’yyar da ke bai wa mata damar neman ko wacce irin kujera kyauta ba tare da sayen fom ba. Mun yi haka saboda muna son mu karfafa musu gwiwa,” inji Damagum.
A yayin gabatar da jawabin maraba da baki, Shugabar Matan Jam’iyyar PDP, Amina Divine Arong ta ce, dimokuraɗiyya za ta ƙara armashi ne muddin aka zaɓi karin mata a mukamai na siyasa.
“Abin baƙin ciki ne yadda aka bar mata a baya duk kuwa da irin rawar da suke takawa wajen samar da sauyi a fagen siyasa,” inji Arong.