A bai wa Rohingya matsayin ’yan kasa – Majalisar dinkin Duniya
Sakatare-Janar n a Majalisar din kin Duniya ya ce Gwamnatin Myanmar ta bai wa Rohingya matsayin ’yan kasa ko tanadin dokar amincewa da su a jerin mutanen kasar, don haka kasashen Musulmi da dama sun ya ba mata kan shirinta na taimaka wa Musulmin Rohingya da suka yi kaura daga Myanmar zuwa kasar Bangladesh, ala’amarin […]

Sakatare-Janar n a Majalisar din kin Duniya ya ce Gwamnatin Myanmar ta bai wa Rohingya matsayin ’yan kasa ko tanadin dokar amincewa da su a jerin mutanen kasar, don haka kasashen Musulmi da dama sun ya ba mata kan shirinta na taimaka wa Musulmin Rohingya da suka yi kaura daga Myanmar zuwa kasar Bangladesh, ala’amarin da ya baibaye kafafen yada labaran duniya a makon jiya.
Rahotanni sun ce Majalisar dinkin duniya da abokan hadin gwiwarta sun shirya kai agaji ga Musulmin Rohingya dubu 300 da suka yi hijira zuwa Bangladesh, inda za a rika ba su wurin kwana da ruwan shad a kula da lafiya da sauran bukatun rayuwa har zuwa karshen wnanan shekarar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na MENA ya ruwaito.
Majalisar ta tura ma’aikatanta zuwa garin Cod Bazar ta inda Robnhingya ke shigowa Banhgladesh, inda ta fitar da kudi Dla miliyan bakwai daga asusun daukin gagawa, yayin da abokan hadin gwiwarta za su fara tallafa wa wadanda ke fama da matsananciyar bukata.
Rahoton ya yi karin haske kan yadda Sakatare-Janar Antonio Guteres ya yi kira ga Gwmanatin Myanmar da ta yi kokarin shawo kan “matsanancin tashin hankalin da ya karade al’umma,” kuma ka da ta yi wata-wata wajen sauya tsarin da aka dade a kai, ta yadda ko dai ta bai wa Musulmin Rohingya kimar matsayin ’yan kasa ko a kimanta matsayinsu bisa tanadin dokar amincewa da su a jerin mutanen kasar.
Shi ma Shugaban addinin Buddha na Duniya Dalai Lama ya yi kira ga shugabar farar hula Myanmar, da ta yi kokarin warware rikicin cikin ruwan sanyi, inda ya nuna damuwarsa kan yadda aka tursasa wa Musulmi har dubu 300 suka bar kasarsu ta haihuwa.