A bar jama’a su zabi shugabannin da suke so a kananan hukumomi – Sarkin Yawuri

Mai martaba Sarkin Yawuri Dokta Muhammadu Zayyanu Abdullahi ya shawarci gwamnatin Jihar Kebbi ta gudanar da zaben kananan hukumomi tare da barin jama’a su zabi shugabannin da suke so don samun ci gaba a jihar. Wata takarda da aka raba wa manema labarai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na Sarkin, Alhaji Ibrahim […]

A bar jama’a su zabi shugabannin da suke so a kananan hukumomi – Sarkin Yawuri
A bar jama’a su zabi shugabannin da suke so a kananan hukumomi – Sarkin Yawuri

Mai martaba Sarkin Yawuri Dokta Muhammadu Zayyanu Abdullahi ya shawarci gwamnatin Jihar Kebbi ta gudanar da zaben kananan hukumomi tare da barin jama’a su zabi shugabannin da suke so don samun ci gaba a jihar.

Wata takarda da aka raba wa manema labarai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na Sarkin, Alhaji Ibrahim Garba Yawuri ta ruwaito Sarki Zayyanu Abdullahi yana cewa idan gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta bar mutane suka zabi shugabannin kananan hukumomin da suka dace domin jagorantarsu, ta haka ne ’yan siyasa za su san darajar mutane.
Sarkin na Yawuri ya ce gwamnatin Kebbi ta bar ’yan takara su je su nemi kuri’a a wurin jama’a, kamar yadda zaben da ya gabata a kasa baki daya domin sanin muhimmancin jama’a.
Dokta Muhammad Zayyanu Abdullahi ya kuma bukaci al’ummar masarautarsa su zamo masu zaman lafiya, kuma su kasance masu bin doka da oda, su yi biyayya ga sabuwar gwamnatin jihar da yi wa kasa addu’a a kowane lokaci domin sai da zaman lafiya ake iya gidanar da kowane lamari na rayuwa.
Sarkin ya jawo hankalin jama’a a kan su rika sanya ido sosai bisa ga wanda ba su yarda da shi ba, tare da ba da rahoto wadanda hankali bai kwanta da su ba ga sarakuna da hukumomin tsaro.
Sarkin ya ce, irin halin da ake ciki yanzu na rashin zaman lafiya da fashe-fashen bama-bamai da sace-sacen jama’a da rashin tausayi ba komai ne ba illa rashin tsoron Allah, “Kuma wajibi ne jama’a su gyara halayensu a kuma roki Allah gafara Ya ba mu zaman lafiya a wannan kasa tamu,” inji shi.
Dokta Zayyanu Abdullahi ya tunatar da manoma a kan sha’anin noma ganin yadda daminar bana ta zo da matsaloli a wasu wurare, kuma wasu gwamnatoci ba su tarar taki a jihohinsu ba daga tsofaffin gwamnatocin da ta suka shude. Ya ce akwai bukatar manoma su shirya wa noman rani gadan-gadan musamman a Jihar Kebbi da Allah Ya albarkace ta da fadamu masu yawa.