A bar wa Shiyya ta Uku kujerar Gwamnan Neja – Abu Lolo
Mai neman Jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar Gwamnan Jihar Neja a zaben badi Alhaji Abubakar Sani Bello wanda aka fi sani da Abu Lolo ya shawarci al’ummar jihar su martaba tsarin karba-karb da manyan jam’iyyu a jihar suka tsara na ba shiyya ta uku damar fitar da Gwamna a badi. Alhaji Abubakar Sani […]
Mai neman Jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar Gwamnan Jihar Neja a zaben badi Alhaji Abubakar Sani Bello wanda aka fi sani da Abu Lolo ya shawarci al’ummar jihar su martaba tsarin karba-karb da manyan jam’iyyu a jihar suka tsara na ba shiyya ta uku damar fitar da Gwamna a badi.
Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayar da wannan shawarar ce bayan da masu ruwa da tsaki suka kammala taron yadda jam’iyyar za ta samu nasara a zabubbukan badi.Ya ce “Ina son jama’a su yi waiwaye zuwa 1999, inda aka fara tsarin karba-karba daga shiyya ta daya wato kasar Nufawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Injiniya Abdulkadir Abdullahi Kure ya shekara 8. Da ya kammala aka zo shiyya ta biyu wadda ta samar da Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu wanda wa’adinsa zai kare a badi. A wannan karon shiyya ta uku ce za ta samar da Gwamnan da zai gaji wannan, don haka, bai kamata a saba wa wannan tsarin ba.”
Da ya juya kan shirye-shiryen da suke yi domin samun nasarar kwace mulki daga hannun PDP, ya ce zaben cike gurbi na Majalisar Dattawa da aka yi kwanakin baya a tsakanin APC da PDP, ya nuna cewa da izinin Allah za su samu nasara don jama’a sun nuna suna bukatar canji a jihar.
Ya ce,”A kullum jam’iyyarmu ta APC da ni kaina muna samun mutanen da suka nuna a shirye suke mu yi aiki tare da su. Ina tabbatar maka cewa nan ba da dadewa ba za mu yi manyan kamu daga wasu jam’iyyu zuwa jam’iyyarmu sai dai ba zan gaya maka sunayensu ba, idan lokaci ya yi za ka ga wadanda nake nufi. Wadanda suka shigo cikinmu daga wasu jam’iyyun muna aiki tare cikin aminci, kuma muna samun nasarori a shawarwarin da suke ba mu. Kuma da izinin Allah za mu yi aiki da su don samun nasara.”
Alhaji Abu Lolo ya ce akwai manya da kananan kungiyoyin siyasa fiye da 274 a gundumomin jihar da suke yi masa ayyukan sa-kai, suna sadaukar da dukiyoyinsu da karfinsu suna buga hotunan neman takara da kuma tallata manufofin da ya tanada ga al’ummar jihar.
Ya yi kira ga al’ummar jihar musamman matasa su guji aikata duk abin da zai zubar musu da mutunci musamman bangar siyasa da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.